Daga Aliyu Sufyan Alhassa
Ƙungiya Sawaba Initiative for humanitarian Development ta gudanar da taron ta karon farko a jihar Kano, domin tattauna hanyoyin da za a magance cin hanci da rashawa a tsakanin shugabanni.
Ƙungiyar ta jaddada cewar matakin yakar cin hanci da rashawa wani lamari ne da ka iya zama barazana ga goben Najeriya matuƙar ba a kai ga takawa lamarin birki ba.
Hasashen yanayin da za’a tashi da shi gobe talata a Birnin Kano da wasu jihohin Nigeria
Shugaban kungiyar na Kano Comrade Tasi’u Tarauni ya ce ƙungiyar tana da rassa a sassan jihohin Najeriya, inda kuma za su gudanar da taro makamancin wannan a jihohin don tabbatar da an samu raguwar cin hanci da rashawa a tsakanin al’ummar Najeriya.
Abubuwan da ya kamata yan Arewa su yi don amfana da mulkin Tinubu – Kwankwaso
Taron ya samu halartar shugaban hukumar karɓar korafi da yaki da rashawa ta jihar Kano Barrister Muhuyi Magaji Rimin Gado, da shugaban hukumar EFCC mai kula da shiyyar kano da Jigawa, sai wakilcin kwamandan hisba na jihar Kano Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa da wakilin Kwamishinan yan sanda na Kano da makamantansu.