Gwamnan Kano Ya Ba Da Umarnin Biyan Masu Sharar Titi Haƙƙoƙinsu

Date:

Daga Hafsat Lawan Sheka

 

Bayan shan ce-ce-ku-ce kan zargin masu shara a Jihar Kano na cewa gwamnatin ta riƙe musu alawus ɗinsu, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ba da umarnin a biya su cikin gaggawa.

A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, Gwamnan ya umarci ma’aikatar muhalli da kula da tsafta (REMASAB) ta tabbatar da biyan duk wasu kudaden alawus-alawus na masu shara da suka gada daga gwamnatin da ta gabata.

Baya ga haka, Gwamnan ya ƙaryata jita-jitar shirin gwamnatinsa na korar ma’aikatan, ya ce ba shi da niyyar hana ma’aikatan da ba su yi laifin komai ba abin dogaro da kai.

Iftila’i: Gobara ta Tashi a Gidan Tsohon Gwamnan Jihar Kano

Gwamnan ya bayar da wannan umarni ne a ranar Lahadi yayin wata ganawa da wakilan masu sharar a gidan gwamnati.

Ya nuna rashin gamsuwa da jinkirin biyan wasu kuɗaɗe bayan amincewarsa.

A cewarsa, “Ban ba da umarnin korar wani daga cikinku ba, maimakon haka ma, mun ɗauki karin ma’aikatan ne domin muhallanmu su kasance cikin tsafta.

“A matsayinmu na ’yan ƙasa na gari, wace fa’ida zan samu kuma wane daɗi zan ji idan na sallame ku daga abin da kuke yi kuke samun abincin yau da kullum?

Abubuwan da ya kamata yan Arewa su yi don amfana da mulkin Tinubu – Kwankwaso

“Wannan taron ya zama wajibi bisa la’akari da kukan da ake yi a kai a kai da kuma labaru marasa daɗi da nake samu saboda rashin biyan ku alawus-alawus din ku.

“Ina mai tabbatar muku da cewa za ku karɓi alawus dinku nan ba da jimawa ba, mun gano inda matsalar take kuma mun gano yadda za mu kawo karshenta”

Gwamnan ya bayyana shirin gwamnatinsa na sayo manyan motoci masu ɗauke da kayan aiki na zamani (Bocket lifters) domin sauƙaƙa kwashe sharar ba kawai daga tituna ba har ma daga lunguna da saƙunan jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...