Clever Warriors sun lashe tikitin shiyyar Kano na Gasar Matasa ta NLO ta Shekarar 2024

Date:

Daga  Musbahu Bala Cediyar Yan Gurasa

 

Mai hoars da kungiyar kwallon kafa ta Clever Warriors FC Bashir lemy Adede ya jagoranci Yan wasan kungiyar har suka zama zakara a shiyyarr kano.

A wani salon wasa mai dauke da gagarumar nasara mai kayatarwa tare da kuma jajircewa, Bashir Adede da Yan wasan na clever sune zasu wakilci shiyyar Kano na Gasar New year Mega Lottery NLO 2024, wanda aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha dake Kano.

Clever Warriors ta samu nasarar zama zakaran gasar ne, bayan ta lashe dukkan wasanni ukun da ta buga a zagaye na biyu.

 

Yadda suka taka leda cikin salon gogewa da hazaka da jajircewar da nuna sadaukarwa ya taimaka matuka wajen wannannan nasarar.

Gwamnatin Kano ta Magantu Kan Harbin Da Aka Yiwa Wani Dan Jarida a Gidan Gwamnatin jihar

kungiyoyin kwallon kafa da suka halarci gasar sun baje kwarewar su danan daban inda Daga bisani dai Clever Warriors suka yi fice a matsayin ‘yan wasan da suka yi fice a duk gasar.

A wasan farko na ranar karshen. a ranar Asabar 4 ga watan Afrilu 2024, Kwankwasiyya FC ta sha kashi da ci 1-4 a hannun Tawayiyya FC.

A wani wasan kuma kungiyar ta Kano Stars ta sha kashi da ci 0-2 a hannun ‘yan wasan Clever Warriors kwallayen masu ban sha’awa, wadanda suka tabbatar da matsayinsu na Daya na gasar shiyyarr Kano da maki 9.

Clever Warriors karkashin jagorancin mamallakin kungiyarDakta Najib Sabo Kurawa sun yi fice a duk gasar, inda suka yi nasara a wasanni 6 sannan suka yi canjaras 2 daga cikin 8 da suka buga gaba Daya.

Zargin Kisan Kai: Rundunar Sojin Sama ta ba da umarnin bincikar yadda Wasu Sojoji suka kashe wani matashi da duka a Kano

Babban Mai hotas da Yan wasan kungiyar Bashir Adede Lemi ya yabawa ‘yan wasansa bisa bajintar da suka nuna, sadaukarwa, da juriya a filin wasa. Ya kuma jaddada kudirin kungiyar na ganin sun cimma burinsu, inda babban burinsu shi ne daukaka matsayin kungiyar matakin gaba wato zuwa ga gasar NNL gasa Mai daraja ta biyu.

Da wannan nasara, Clever Warriors za su tsallake zuwa wasannin fidda gwani Play-Off, don karawa da kungiyar da tayi nasara a shiyyarr Dutse a ranar 27 ga Mayu a garin Daura, dake Jihar Katsina.

Taimako da kyakkyawan jagoranci da Dakta Najib Sabo Kurawa ya bayar tare da kwazon ’yan wasa da kuma kwazon ’yan wasa da masu horaswa ya sanya Clever Warriors suka zama zakara a shiyyar Kano.

Yadda Magoya baya da masu bibiyar wasanni a shiyyarr ya Karawa yan wasan mu karsashi a lokavin da suke taka kwallo a gasar ta bana .

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...