Akalla ƴan jaridu 20 aka Kai wa hari a Najeriya cikin 2023 – Rahoto

Date:

Ƙungiyar kare ƴan jarida ta duniya ta ‘Reporters Without Borders’ ta ce kimanin ƴan jaridu 20 ne aka kai wa hari cikin shekara ta 2023 a Najeriya.

Hakan na ƙunshe ne a wani rahoto da ƙungiyar ta fitar a daidai lokacin da ake bikin ranar kare hakkin ƴan jaridu ta duniya.

Rahoton ya ce siyasa ta taka muhimmiyar rawa wajen ci gaba da cusguna wa ƴan jarida a nahiyar Afirka, musamman a ƙasashe irin Najeriya, inda aka gudanar da zaɓen shugaban a shekarar ta 2023.

A yanzu haka Najeriya ce ta 112 a jerin ƙasashen duniya kan batun ƴancin ƴan jaridu .

Hajjin Bana: NAHCON ta bayyana ranar da zata fara jigilar alhazan Nigeria

Haka nan rahoton ya ce a lokacin zaɓen na Najeriya ƴan siyasa sun yi ƙoƙarin amfani da damarsu wajen murƙushe kafafen yaɗa labaru, yayin da wasu ƴan siyasar kuma suka kafa nasu gidajen yaɗa labarun domin yaɗa fargfaganda.

Rahoton na ƙungiyar kare ƴan jarida ta duniya ya bayyana cewa Gabas ta tsakiya ne yankin da aka fi cin zarafin ƴan jarida a faɗin duniya.

Rahoton ya ce “yanayin ya munana” a kusan rabin ƙasashen yankin Gabas ta tsakiya.

NAWOJ ta yi alkawarin hada kai da ma’aikatar tsaro don magance ta’addanci a Nigeria

Ƙasashen da lamarin ya fi ƙazancewa su ne: Yemen, Saudiyya, Iran, Yankin Falasɗinawa, Iraƙi, Bahrain, Syria da Masar.

Yankin Falasɗinawa shi ne wuri mafi haɗari ga ƴan jarida a faɗin duniya, kuma tana cikin ƙasashe na can ƙasa a ɓangaren kare ƴan jarida a duniya.

Ƙasashen da ƴan jarida suka fi samun ƴanci da sauƙin gudanar da ayyukansu kamar yadda rahoton ya nuna kuwa sun fi yawa ne a nahiyar Turai.

Ƙasa ta farko ita ce Luxembourg, sai Liechtensein a matsayi na biyu, yayin da Samoa take a matsayi na uku.

BBC Hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...