Mafi Ƙarancin albashi: Kungiyar Kwadago ta bai wa gwamnatin Tinubu sabon wa’adi

Date:

Daga Isa Ahmad Getso

 

Ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya ta bai wa gwamnatin ƙasar nan da 31 ga watan Mayu don ƙara fito da sabon albashi mafi ƙaranci ga ma’aikatan ƙasar.

Ƙungiyar ta sanar da haka ne yayin bikin murnar ranar ma’aikata ta ƙasa a filin taron Eagle Square da ke Abuja a ranar Laraba.

Shugaban ƙungiyar NLC Joe Ajaero tare da takwaransa na ƙungiyar TUC Festus Osifo sun haɗu kan cewa mafi ƙaranci albashi na naira 30,000 ya yi wa ma’aikatan Najeriya kaɗan duba da yanayin matsi da kuma tsadar rayuwa da ya haɗa da tashin farashin abinci da kuɗin wuta da na sufuri da kuma sauransu.

Auren Zawarawa: Hisbah ta Baiwa Yan Jaridu Gurbin mutane 50

Sun dage kan naira 615,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi da suke so gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta saka hannu kafin ƙarshen watan Mayu.

Ajaero ya ce, “ƙungiyar NLC da ta TUC na jaddada cewa matsawar za a ci gaba da tattaunawa kan batun mafi ƙarancin albashi ba tare da mafita ba har zuwa ƙarshen Mayu ba za mu iya ci gaba da ba da haɗin kai ba a ƙasar nan”.

Tinubu ya karawa ma’aikatan Nigeria albashi

A ɓangaren Osifo kuma ya nemi hukumar kula da wutar lantarki tare da kamfanonin da suke rarraba wutar kan su janye ƙarin kuɗin da su ka yi wa mutane da ke rukunin A waɗanda suka fi samun wuta.

Ƴan Najeriya sun tsinci kansu cikin raɗaɗin tsadar rayuwa da layi mara iyaka a gidajen mai bayan tashin farashi da rashin man fetur a fadin ƙasar.

Duk da tabbacin da kamfanin mai na ƙasa ya bayar kan shawo kan matsalar, an ci gaba da samun layuka a gidajen siyar da mai fiye da tsawon sati ɗaya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Tinubu ya Iso Kano domin ta’aziyyar Dantata

Shugaban Nigeria Bola Ahmad Tinubu ya iso jihar Kano...

ALGON ta Kano Sa’adatu Soja ta sami sabon matsayi a kungiyar ALGON ta Ƙasa

Daga: Aliyu Danbala Gwarzo. Shugabar karamar hukumar Tudunwada kuma ALGON...

Da dumi-dumi: Tinubu zai zo Kano

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu zai zo Kano ranar...

Tinubu ya sauya sunan jami’ar Maiduguri zuwa Sunan Muhd Buhari

Shugaba Bola Tinubu ya sauya sunan Jami'ar Maiduguri zuwa...