Titin Kano zuwa Maiduguri ya Zama Tarkon Mutuwa – Sanata Kawu Sumaila

Date:

Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa

 

Sanatan Kano ta kudu a majalisar dattawan Nigeria Sulaiman Kawu Sumaila, ya bayyana babbar hanyar Kano zuwa Maiduguri a matsayin tarkon mutuwa da ke lakume rayukan al’umma masu yawa dake binta.

Kadaura24 ta rawaito Kawu Sumaila ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Kano, ranar Lahadi.

Ya jajanta wa iyalan mutane 11 nan, wadanda suka rasa rayukansu a wani hatsarin mota da ya rutsa da su a kan babbar hanyar da take ta gwamnatin tarayya ce, a ranar Juma’ar da ta gabata.

Yanzu-yanzu: Gwamnatin Kano ta Rufe Wani Asibiti Mai Zaman Kansa Saboda Karya Doka

Ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ce ta bayar da kwangilar aikin biyu na titin sama da kilomita 550, a karshen wa’adin mulkin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo na biyu.

” Wannan hanyar ya na da muhimmanci sosai wajen ci gaban tattalin arzikin Najeriya, domin hanyar ta hada Najeriya da kasashen Jamhuriyar Chadi, Kamaru, Nijar da Afirka ta Tsakiya, ta yadda hakan ke kara habaka kasuwanci a tsakanin jama’a. kasashen”. A cewar Kawu Sumaila

Ya kuma ce hanyar da ta hada Kano da Jihohin Jigawa da Bauchi da Gombe da Yobe da kuma Borno na taka rawar gani sosai a harkokin ci gaban tattalin arzikin jihohin.

Kotu Ta Jingine Dakatarwar Da Aka Yi Wa Ganduje

Sai dai duk da wannan mahimmancin, dan majalisar ya ce hanyar ta yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama sakamakon rashin kammala aikin.

Ya ce kusan shekaru 17 da bayar da kwangilar aikin, amma har yanzu ba a kammala wani kaso na hanyar musamman daga Wudil zuwa Gaya ba.

“Abin takaici ne duk da cewa an kammala sama da kilomita 50 na wannan bangare na hanyar, ba a kammala kasa da kilomita 30 na bangaren ba, wanda hakan ya haifar da hadurra a tsakanin masu ababen hawa dake bin hanyar”, in ji shi.

Sumaila ya nuna damuwa kan yadda rashin kammala aikin ya sanya ‘yan kasuwa a cikin Najeriya da makwaftan kasashen da ke makwabtaka da Kano suke karkatar da harkokin kasuwancinsu zuwa wasu jihohin .

Don haka ya yi kira ga ma’aikatar ayyuka da gidaje ta tarayya da dan kwangilar da ke tafiyar da aikin da su tabbatar da kammala aikin hanyar domin ceto rayukan al’umma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...

Dalilin Kwankwaso na kin shiga Hadakar ADC

Jam'iyyar NNPP ta ce abin da ya sa ba...