Daga Husna Yusuf Deneji
Jarumar fina finan Hausa na Kannywood Asmau Wakili wadda aka fi sani da Asmee Wakili ta bayyana cewar ba za ta iya zama da duk wanda ba ya son sana’ar da take yi ba.
Jarumar ta bayyana hakan ne a cikin wani bidiyo da ta wallafa a shafinta na TikTok, kamar yadda jaridar leadership ta rawaito.
CBN ya bayyana matakan da yake bi har Dala take karyewa a Nigeria
Wasu na kallon sana’a fim a matsayin wata sana’a da ba za su iya zaman aure da duk wani wanda yake cikin harkar ba, hakan ya sa jarumai a masana’antar kan fito fili su nuna cewa suma haka abin yake a wajensu domin kuwa kowa tashi ta fishshe shi.
Asmee Wakili jarumar Kannywood ce wacce ta shahara a wannan kafa musamman fannin raye-raye inda take fitowa a manyan fina finai tana tikar rawa tare da abokan aikinta, hakan ya sa ta tara dimbin masoya masu shaawar kallon wakokin da take fitowa a cikinsu.