Shugaban IPMAN a Kano ya bayyana dalilin samun layin Ababen hawa a gidajen mai

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Mazauna jihar kano sun Kasance cikin ruɗani sakamakon yadda suke fuskantar ƙarancin man fetur a kwaryar birnin jihar.

Jaridar BizPoint ta rawaito cewa yawancin gidajen man yan kasuwa dake kwaryar birnin Kano sun kasance a rufe.

Hakazalika, bincike ya nuna cewa akwai layukan da ake samu a wasu gidajen man da suka bude domin sayar da man fetur a cikin birnin, musamman ma gidajen man NNPC.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da farashin man fetur din ya tashi daga N690 zuwa Naira 730 kan kowace lita, hatta a manyan gidajen man‘yan kasuwa.

Wakilin majiyar kadaura24 da ya zagaya wasu gidajen mai a birni na biyu mafi yawan jama’a a Najeriya, ya lura cewa akwai layukan matoci da sauran Ababen hawa a wasu gidajen man.

Rundunar yan Sanda ta tsare jami’anta da ke gadin tsohon gwamnan Kogi Yahaya Bello

Gidan man Aliko Oil da ke kan titin Maiduguri a Kano, an same shi cike makil da ababen hawa a ciki da wajen harabar gidan man, lamarin da ya haifar da dan takaitaccen cunkoson ababen Hawa a titin Sabo Bakin zuwo da sauran hanyoyin da ke kewayen gidan man

Hakazalika, a gidan man A. Y. Maikifi da ke kan titin, dan jarida ya lura cewa akwai dogon layin sosai a gidan man har zuwa waje.

Wani direban mota mai suna Muhammad Usman ya ce ya zagaya wurare da dama domin neman mai amma bai samu ba sai da ya zo gidan A. Y. Maikifi .

A cewar Usman, ya rasa dalilin da ya sa aka rufe akasarin gidajen man sannan aka sake samun dogayen layi a wuraren sayar da man fetur.

Wanda ya kafa jam’iyyar NNPP ya bayyana yadda yake zargin Kwankwaso da cin amanar sa

Shi ma wani direban mota mai suna Suleman Haruna ya ce ya dauki tsawon sa’o’i yana kokarin siyan man fetur din a wani gidan mai a hanyarsa ta zuwa gona.

Kamar Usman, Haruna ya bayyana mamakin dawowar dogayen layukan ababen hawa ba zato ba tsammani duk da cire tallafin man fetur.

Da aka tuntubi shugaban kungiyar dillalan man fetur ta kasa IPMAN reshen jihar Kano, Alhaji Gana Girgire ya ce karancin man fetur din ya biyo bayan hutun sallah da direbobin tankar man fetur suka yi.

A cewarsa, direbobin tankar da ke jigilar man zuwa wasu wurare a fadin kasar nan daga Legas, suna hutun Sallah, amma nan ba da jimawa ba za su ci gaba da aiki.

Shugaban ya kuma alakanta karancin man da yadda wasu ‘yan kasuwa basa iya sayo man daga Legas saboda karin farashinsa da aka samu.

A cewar Girgire, “yan kasuwar yanzu haka suna samar da man fetur a kan Naira 640 kan kowace lita daga Legas. Za su biya Naira 50 kudin sufuri a kowace lita. Nawa kuke tsammanin za su sayar da shi a gidajen mansu?.

“Wannan shi ne dalilin da ya sa akasarin ‘yan kasuwa suka daina samar da kayan don gujewa tafka asara. Wannan shi ne dalilin da ya sa farashin man fetur ya kai Naira 730 kan kowace lita.

“Amma akwai wasu da suke sadaukarwa don samar da man akan wannan farashin. Amma wadannan su ne manyan dalilan karancin man a jihar Kano,” inji shi.

Shugaban ya kuma ce lamarin ba a Kano ne kadai ba, har ma da wasu sassa da dama a Arewacin Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...