Sojojin Nigeria Sun Hallaka ’Yan Bindiga 11 A Katsina Da Zamfara

Date:

Dakarun Sojin Najeriya sun kai samame wasu maboyar ’yan bindiga a jihohin Katsina da Zamfara, inda suka yi nasarar kashe 11 daga cikinsu.

Wannan na cikin wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafinta na X (Twitter), a ranar Litinin.

Rundunar ta ce a wani samame da suka kai a Zamfara a ranar 29 ga watan Maris, sun yi nasarar tarwatsa maboyar kasurgumin dan bindiga, Hassan Yantagwaye, a Karamar Hukumar Tsafe.

Gwamnatin Kano Ta Kori Wasu Ma’aikatan Lafiya 3, TA Kuma Dakatar Da Wasu

Sanarwar ta kara da cewa, Yantagwaye da yaransa ne ke da alhakin sace mutane da ayyukan ta’addanci a wasu yankunan Arewa maso Yammacin Najeriya.

“A yayin farmakin, sojoji sun fatattaki ’yan bindigar a wani artabu da suka yi, inda suka kashe uku daga cikinsu tare da kwato muggan makamai da alburusai a maboyarsu.

Sarkin Kano ya Jagoranci Rabawa Marayu Kayan Sallah da Gidauniyar Hasken Al’umma ta Samar

“A Jihar Katsina kuwa, a ranar 30 ga watan Maris, sojoji sun yi artabu da ‘yan bindiga a yankunan Shawu Kuka, Shinda, Tafki, Gidan Surajo, da Citakushi a Kabai I da Kabai II duk a Karamar Hukumar Faskari.

“Sojojin sun kashe ’yan bindiga takwas tare da kwato bindigogi guda uku kirar gida, kakin soji da kuma kayan abinci,” in ji sanarwar.

Rundunar ta ce tana ci gaba da yaki da ’yan ta’adda domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a jihohin da ma Najeriya baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...