Gwamnatin Kano Ta Kori Wasu Ma’aikatan Lafiya 3, TA Kuma Dakatar Da Wasu

Date:

Daga Halima Musa Sabaru

 

Hukumar kula da asibitocin jihar Kano ta amince da korar wasu ma’aikata tare da dakatar da wasu ma’aikatan na babban asibitin Karamar Hukumar Kabo nan take, bayan samunsu da lefin Cazar kudade daga marassa lafiya da suka wuce Kima da sauran lefuka.

Asibitin wanda babban sakataren hukumar da babban darakta na cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa ta jihar Kano (KNCDC) Dr. Muhammad Abbas, da darakta janar na CSACA Dr. Usman Bashir suka ziyarce su gaba daya sun nuna bacin ransu ga abinda ya faru tare da amincewar daukar matakin.

Shugaban hukumar Dakta Mansur Mudi Nagoda ya bayyana hakan jim kadan bayan sanya hannu kan amincewar da hukumar ta gabatar bayan kammala ziyarar da suka yi a asibitin.

Dakta Nagoda ya yi bayanin cewa an kama jami’ai 3 na sashen X-ray suna cajin marasa lafiya 12,000 na gwajin X-ray maimakon farashin asibiti da aka amince da shi na 2,000 kuma babu wata takarda da za ta nuna a matsayin shaidar biyan kuɗin da ke barin wurin don aiwatar da gwajin, lamarin da yasa ake X-ray 10 kacal a kowanne mako duk da cewa Injinan Asibitin na X-ray 2 suna aiki.

Dalilin Da Yasa Yin Sallar Tahajjud A Gida Ya Fi Lada —Sheikh Ibrahim Khalil

Daga nan sai ya amince da korar jami’an 3 nan take.

Har ila yau, shugaban Hukumar ya amince da dakatar da akawun Asibitin da mai binciken kudi da shugaban dakin gwaje-gwaje saboda sayar da kayan gwajin cuta mai karya Garkuwar jikin Dan Adam wanda kyauta gwamnatin jihar ta ba wa cibiyoyi kuma an umarce su da su kai kansu ga hedikwatar hukumar don ci gaba da ladabtar da su.

Bugu da kari, Dakta Nagoda ya bayyana cewa dakin karbar Haihuwa na Asibitin ba shi da tsari domin ba shimfidar gado a kan gadaje, babu wani jami’in kula da gurin, haka kuma an wulakantar da wasu kayayyakin kula da lafiyar Alumma wanda wani majalisa ya bayar da gudummawar shekaru 4 da suka gabata, tare da nuna halin ko in kula da kayayyakin yaki da cutar COVID-19.

Rikicin UBA Sani Da El-Rufa’i Ya Fara Tafiyar Ruwa da Mukaman Wasu a Kaduna

Shugaban ya kuma ce abin bakin ciki ne bayan mai girma gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf ya tabbatar da cewa ya dawo da kowane ma’aikacin lafiya a kan ma’aunin albashin CONHESS, amma duk da haka suna cin zalin Marassa Lafiya tare.

Jami’ar hulda da jama’a ta hukumar Samira Suleiman ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa a Kano ranar Lahadi.

Sanarwar ta ce shugaban ya yi kira ga maaikatan hukumar da su rika gudanar da ayyukansu don cigaba da kula da lafiyar Alummar Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...