Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Kungiyar samarin Tijjaniyya ta bayyana nadin da shugaban kasar Najeriya yayi wa Ritaya Janar Lawal Jafaru Isa Kano da Dr. Sani Muhammad Idris Yobe da cewa abu ne da zai kara inganta harkar ilimin addini Musulunci a Kasar nan.
Jawanin hakan ya biyo bayan wata sanarwar da kungiyar Samarin Tijjaniyya ta kasa ta fitar mai dauke dasa hannun Babban Sakataren kungiyar na kasa Shehu Tasi’u Ishaq da Babban Jami’in yada Labaran Kungiyar na Kasa Abubakar Balarabe Kofar Naisa.
Kungiyar RATTAWU ta ARTV ta zabi sabbin shugabanninta
Sanarwar yace idan akayi la”akari da irin gudunmawar da wadannan mutane biyu suka bayar wajan cigaban addinin Musulunci da inganta makarantun tsangayu Shugaba Tinibu yayi namijin kokari da hangen nesa wajan basu wadannan mukamai.
Sai dai kuma Kungiyar Samarin Tijjaniyyar ta Kasa taja hankalin wadanda aka bawa wadannan mukamai suyi aiki tsakaninsu da Allah bisa amana da gaskiya kamar yadda aka sansu tareda nuna rashin banbanci ko bangaranci domin ciyar da Kasar nan gaba.
Ramadan: NAWOJ ta Shiryawa Yan Jaridu Mata Lacca a Kano
Sanarwar ta yabawa Shugaba Ahmed Bola Tinibu bisa yadda yake nada mukamai ta hanyar zabo jajirtattu da kuma ajiye kowa a gurbinsa wanda ya kware a fannin da yake domin gudanar da aikin cigaban Kasa.
Daga nan Kungiyar Samarin Tijjaniyyar tayi kira ga yan Najeriya su cigaba da yiwa wannan Kasar aduu’ar samun zaman lafiya da karuwar arziki da dorewar tattalin arziki da kuma samun cikakken tsaro musamman a wasu jihohi da ake fama da tabarbarewar tsaro.
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito Shugaban ƙasa ya amince da nada Lawan jafaru Isa a matsayin shugaban hukumar gudanarwar hukumar, sannan ya nada Dr. Sani Muhammad Idris a matsayin Sakataren zartarwar na hukumar, bayan cire Sha’aban Ibrahim Sharada.