Daga Nasiba Rabi’u Yusuf
Wasu da ake zargin masu yawon ta zubar ne sun tsallake rijiya da baya, bayan gobara ta tashi a otel din mairabo da suke shakatawa a unguwar Sabon gari dake karamar hukumar Fagge a jihar kano
Rahotanni sun tabbatar da cewa an garzaya da wasu mutane hudu zuwa Asibiti a daren jiya bayan sunji raunika, a sakamakon fadowa ta taga daga kan benen otel din mai hawa uku dake kan titin Aitken a yankin sabon gari .
Kantomomi: Kotu ta baiwa gwamna da majalisar dokokin jihar kano Umarni
Majiyar mu ta baiyana mana cewar mutanen hudu sun hada da maza biyu da mata biyu, wanda suke tsaka da shakatawa a cikin dakunan dake otal din, a lokacin da gobarar ta tashi, lamarin da ya tilasta masu fadowa daga kan tagogin otal din zuwa kasa, kamar yadda aka gani cikin wani faifan bidiyo.
Da Dumi-Dumi: Tinubu Ya Baiwa Dan Ganduje Mukami
Rahotanni sun bayyana cewa gobarar ta tashi ne sakamakon wutar lantarki wanda yasa daya daga cikin na’urorin sanya wurin ya kama da wuta.
Jami’an yan sanda da kuma jami’an kashe gobara sun yi gaggawar zuwa wurin da lamarin ya faru domin kashe wutar, kuma zuwa yanzu dai babu rahoton samun asarar rai.
Arewa Radio