Kantomomi: Kotu ta baiwa gwamna da majalisar dokokin jihar kano Umarni

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Babban kotun tarayya dake zamanta a jihar kano karkashin jagorancin mai shari’a M A Liman ya umarci gwamnatin jihar da majalisar dokokin da su dakatar da shirinsu na nada Kantomomi a kananan hukumomi jihar 44.

Hakan na kunshe ne cikin wata takardar Umarni da kotun ta fitar mai dauke da umarni kusan 4, wacce take dauke da kwanan watan 7 ga watan maris, 2024.

A ciki Karar da wani Haruna Abbas Babangida ya shigar, alƙalin kotun ya kuma umarci babban akanta na kasa da babban lauyan kasar nan kuma ministan Shari’a da kada su sake gwamnatin tarayya ta sakawa kananan hukumomin jihar kano kudaden wata-wata muddin aka nada Kantomomi har sai an kammala sauraren Shari’ar.

Kotun dai ta umarci dukkanin bangarorin da kowa ya tsaya a Inda yake har sai kotun ta gama sauraron Shari’ar.

Yadda Herbert Ya Ceci Iyalaina Lokacin da Ganduje Ya Cire Ni Daga Sarkin Kano –Muhammad Sanusi II

Wanda yayi karar Haruna Abbas Babangida ya bukaci kotun da ta dakatar da gwamnati da majalisar dokokin jihar kano daga nada Kantomomi, sannan kuma kotun ta baiwa babban akanta na kasa Umarnin kada su turawa Kantomomi kudaden kananan hukumomi saboda ba zababbu bane.

Yace nada Kantomomin ya sabawa tsarin dimokaradiyya.

Kano: KNUPDA ta Kama Mutane 6 bisa karya dokokin hukumar

Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito a ranar litinin gwamnan jihar kano Abba Kabir Yusuf ya turawa majalisar dokokin jihar wasikar nema majalisar ta Amince masa ya nada Kantomomi a kananan hukumomi 44 sakamakon karewar wa’adin zababbun shugabannin kananan hukumomin a ranar 12 ga watan da ya gabata.

A jiya dai majalisar ta bada sanarwar ta kammala aikin tantance sunayen shugabannin riko na kananan hukumomin da gwamnan jihar kano ya tura musu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dr. Kabiru Getso Ya Mika Ta’aziyya Ga Iyalan Buhari

Daga Rahama Umar Gwaru   Tsohon kwamishinan ma'aikatun lafiya da muhalli...

Gwamnatin tarayya ta ayyana Ranar hutu saboda rasuwar Buhari

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ayyana Talata, 15 ga watan...

Injiniya Iliyasu Usman Salihu ya zama Jakadan zaman Lafiya na Africa

    Injiniya Ilyasu Uasman Salihu, Manajan Darakta na Sadex Engineering...

Halin da ake ciki game da shirye-shiryen jana’izar Buhari

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya bayayna cewa sai...