Yadda al’ummar Karamar hukumar T/Wada sun gudanar da addu’o’i ga wadanda aka kashe a zaɓen 2023

Date:

Daga Aliyu Danbala Gwarzo

 

Bayan cika shekara 1 da gudanar da babban zabe a Nigeria al’ummar karamar hukumar tudun wada a jihar kano sun gudanar da taron addu’o’i na musamman ga wadanda suka rasa rayukansu da kuma ziyartar wadanda suka jikkata bisa iftila’in da faru a zaben shekarar 2023 a yankin.

Shugaban karamar hukumar tudun wada na riko tare da mukarra bansa ne suka jagoranci gudanar da taron, inda suka nuna rashin jin dadinsu da afkuwar lamari tare da jajantawa iyalan wadanda suka rasu da kuma wadanda suka samu raunika.

Da dumi-dumi: Kotu ta sake bada sabon Umarni akan Mawaki Ado Gwanja

Taron ya gudana a sakateriyar karamar hukumar tudun wada a ranar litinin 26 ga watan fabrairun shekarar da muke ciki.

Da yake jawabi a yayin taron tsohon Dan majalisar dokoki ta jihar kano da ya wakilci karamar hukumar Hon. Abdullahi iliyasu yaryasa yace “hakika bazamu taba mantawa da wanan rana ba saboda rana ce mafi muni a wannan gari duba da wannan iftila’in daya samemu a irin wannan rana dan haka ba zamu manta wannan alamari ba”.

Yan Sanda Sun Kama mutane 9 Masu Chanjin kudaden Waje ba Bisa ka’ida ba

“Muna godiya ga limamai da malamai har ma da al’ummar da suka fito domin gudanar da addu’oin tare da rakiya izuwa gidajen wadanda suka rasu da wadanda suka samu raunika a wancan rikici”.

Kazalika Hon. Yaryasa yace suna kira ga gwamnatin jihar kano da ya duba wannan lamari a yiwa al’ummar tudun wada adalci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Abubakar Bichi ya bada gudumawar motocin bas 13 ga jami’o’in Kano da taraktoci 11 ga yan mazabarsa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar...

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...