Gwamnatin mulkin sojin Nijar ta ce ta kayade farashin kudin shinkafa a kasuwanin kasar.
Gwamantin tace bayan dogon bincike da ta gudanar tsakanin masu ruwa da tsaki ta tsayar da farashin duba da yadda ba inda ake sayar da shinkafa sama da CFA Jika 13.
Da dumi-dumi: Bayan Zanga-Zangar Masu Shara a Kano, Danzago ya koka
Cikin wata sanarwa da ministan harkokin kasuwanci na kasar ya sanya wa hannu, ya gwamnatin kasar ta dauki matakin karyar da farashin shinkafar da ake shigar da ita cikin kasar.
Sanarwar ta kuma kayyade sabon farashin da za a rika sayar da shinkafar a fadin kasar, daga jaka 16 da rabi ko 17, zuwa jaka 13 da rabi ko 14 a wasu jihohin kasar,
Farashin shinkafar a kuɗin Nigeria ya kai 40,800, zuwa 38,400 ko 33,600 ko 31, 200 a farashin Naira.
Gwamnatin ta ce ta dauki matakin ne bayan tuntubar ‘yan kasuwa da masu saye da sauran masu zirga-zirgar sufurin da sauran masu ruwa da tsaki.
BBC Hausa