Yanzu-yanzu: Tinubu ya dakatar da ministar jin ƙai, Betty Edu

Date:

Shugaban Kasar  Najeriya, Bola Tinubu ya dakatar da ministar jin ƙai, Betty Edu nan take.

Kakakin shugaban Najeriyar, Ajuri Ngelale ne ya sanar da matakin dakatar da ministar cikin wata sanarwa da aka fitar a yau.

Shugaba Tinubu ya ɗauki matakin ne domin ba da dama ga hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa ta gudanar da bincike a kanta.

Yanzu-yanzu: Kotun Ƙoli ta Yanke Hukunci kan Shari’ar zaɓen gwamnan jihar Benue

Tun farko al’ummar Najeriya sun yi ta matsa lamba inda suke kiraye-kiraye gwamnati ta dakatar da ita daga mukaminta domin a gudanar da cikakken bincike a kanta game da zarge-zargen da ake mata.

Ana zargin ta da bayar da umarnin tura kuɗi kimanin naira miliyan 585 zuwa asusun bankin wata mata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related