Daga Haruna Shu’aibu Danzomo
An Haifi Farfesa a Garin Hadejia Dake Karamar Hukumar Hadejia a Jihar Jigawa a Ranar 26, ga Watan Fabarairu na Shekarar 1967 Farfesa ya fara Karatun sa daga Andulkadir Primary School Dake Hadejia a shekarar 1974 ya Kuma karasa a Sambo Primary School a shekarar 1979 duk a Garin Hadejia daga Nan Farfesa ya Shiga Karamar Makarantar Gaba da Primary ta Maza Dake Garin Hadejia daga 1980-1982 Kuma Babu Bata Lokaci ya wuce zuwa Makarantar Kimiyya Dake Dawakin Kudu a tsohuwar Jihar Kano inda ya kammala a 1985.
Daga nan Farfesa ya Shiga Jami’ar Ahmadu Bello Dake Zaria inda ya karanta Veterinary Medicine a shekarar 1988-1995. Bugu da Kari Farfesa yaci Gaba da Karatun sa a Wannan Jami’ar ta Ahmadu Bello Dake Zaria inda har ya samu Digirin Digirgir akan Wannan fanni na Likitocin Dabbobi wato ( Doctor of Veterinary Medicine DVM ), da Kuma PhD in Veterinary Medicine Baki Daya Daga 1995-2019.
Hakazalika a shekarar 2016 Farfesa ya Halarci Kwas akan cutattukan Dabbobi musamman BOVINE AND HUMAN TUBERCULOSIS MOLECULAR DIAGNOSTICS a Babban asitin Ruti a Spain da Sauran ireiren Su.

Farfesa SALISU IBRAHIM HADEJIA ya rike Mukaman da suka Shafi Harkar gudanarwa Kamar Mukaddashin Shugaba na sassasa Daban Daban da tsangayoyin Ilmuka Daban Daban a Jami’ar Ahmadu Bello Dake Zaria. Hakazalika Farfesa ya zama Member a Kwamatoci da Dama duk Dai a Wannan Jami’ar.
Mafi akasarin Bincike da Kuma rubutuce rubucen Farfesa sun Fi ta’allaka akan Abin Daya Shafi Litancin Dabbobi da Kuma Abin Daya Shafi cutar BOVINE AND HUMAN TUBERCULOSIS EPIDEMIOLOGY Yana Kuma da Rubututtuka sama 45 a Wannan fannin musamman a Cikin Jaridun Gida Nigeria Dama Kasashen Ketere.
Rundunar Yan Sanda ta Kano ta Bayyana Sunayen Mutane 72 da Ta ke Nema Ruwa A Jallo
Farfesa Cikakken Kuma Kwararren Likitan Dabobi ne musamman Abin Daya Shafi cutattukan Shanu Kuma yana Matsayin Babban Likitan Manyan Gonaki da makarantun Dabobi a Nigeria.
Farfesa yana Cikin Babbar Kungiyar Likitocin Dabbobi ta Nigeria.
Farfesa yayi shekara 28 yana aikin likitanci na dabbobi, daga cikin wadanan shekarun, yayi 15 yana koyarwa a jamia, 5 a maaikatar bincike da kuma shekaru 10 a maaikatar aikin gona da kiwo.
Manyan abubuwan da Farfesa yake so sun haɗa da Noman Shanu da Kuma Kallon Kwallon Kafa.
Wallafar
Haruna Shu’aibu Danzomo.