Mun gano Shirin Matasan dake son kona gidan gwamnatin Kano – CP Gumel

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano CP Muhammad Usaini Gumel, ya ce sun samu rahoton wasu bata gari na shirin kona gidan gwamnatin jihar Kano.

Kadaura24 ta rawaito Kwamishinan ya bayyana hakan ne yayin ganawar da yayi da shugabannin kafafen yada labarai da ta gudana a ranar Laraba, a shelkwatar rundunar dake Bamfai.

Talla

yana mai cewa jami’ansu zasu dakile bata garin dake da dabi’ar neman kona gidan gwmnatin Kano.

Ana Tuhumar MD Radio Kano da Cefanar da Wasu Muhimman Kayan Aiki a Tashar

Kwamishinan ‘yan sandan ya ce duba da yadda kotun koli zata fara sauraron karar zaben gwamnan jihar Kano a ranar Alhamis a Abuja, sun lura da yadda wasu bata gari suka fara bin shafukan sada zumunta suna yada labaran karya, a dan haka ya bukaci halatttun kafafen yada labaran da su kauracewa yin amfani da labaran karya da suke yawo a shafukan sada zumunta.

” Ba zamu bari wannan abun ya kasance ba, kuma mun ɗauki koraran matakan da zasu hana faruwar hakan, sannan kuma duk Wanda muka kama shi da kokarin aikata abubuwan da basu dace ba, yayin yanke hukuncin Kotun Ƙoli to zai dandana kudar sa”. CP Gumel

Kwamishina Gumel ya kuma yabawa kafafen yada labarai dake jihar Kano, duba da yadda suke baiwa rundunar hadin kai a ayyukanta na kiyaye rayuka da dukiyoyin al’ummar jahar dama kasa baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Ku ba da gudunmawa kano ta zauna Lafiya – Waiya ya shawarci yan jaridun yanar gizo

Gwamnatin jihar Kano ta bukaci kafafen yada labarai na...

KAROTA ta tabbatar da aniyarta na inganta matsayin jami’anta

Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Jihar Kano...

Sarkin Sanusi ya amince da nadin sabon mai unguwar Hotoro GRA

  Mai martaba Sarkin Kano na 16, Malam Muhammadu Sanusi...