Yan jaridu biyu daga Kano sun lashe zaben gwarazan shekara ta 2023

Date:

Daga Maryam Muhammad Ibrahim

Wasu yan jaridu guda biyu daga jihar kano Shehu Usman Salihu na premier Radio da Jamila Siyoji Adam ta Arewa Radio sun lashe lambobin yabo na gwarzan shekara ta 2023, a ɓangaren gabatar da shirye-shirye da Kuma Karanta labarai.

Shehu Usman Salihu na premier Radio shi ne ya lashe zaɓen gwarzon mai gabatar da shirye-shirye na shekara ta 2023 a ɓangaren maza , yayin da Jamila Siyoji Adam ta Arewa Radio ta lashe zaben gwarzuwar shekara a ɓangaren Karanta labarai a Shekara ta 2023 a ɓangaren mata.

Talla

Wata kungiya ce mai suna Nigerian Radio Award ta shirya Inda yan jaridu daga sassa daban-daban na Nigeria suka shiga gasar Kuma aka yi ta zabe har Allah ya bada nasara ga yan jaridun jihar kano biyu suka lashe zabukan.

Dalilan Rufe Shoprite Dake Kano A Sabuwar Shekara

Dama dai duk shekara kungiyar ta kan shirya irin wannan zabe Inda ake bada dama ga mutanen gari su zabi wadanda suka shiga zabe ta hanyar yanar gizo a ɓangarori daban-daban na aikin Radio

Taron da aka gudanar jiya a Abuja ya sami halartar yan jaridu da dama daga sassa daban-daban na Nigeria.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...