Daga Aisha Aliyu Umar
Tsohon kwamishinan ma’aikatar raya karkara ta jihar kano Hon. Dr. Musa Iliyasu Kwankwaso ya sha alwashin ɗaukar matakin Shari’ar akan duk wanda ya sake cewa za’a kwacewa gwii.mimamna Abba Kabir Yusuf kujerar gwamnan Kano.
” Ta yaya mutanen da kotu ta tabbatar da cewa sun yi aringizon kuri’un bogi har kotun ta kwashe su da kanta ta kuma lissafa ta gano Gawuna ne yaci zabe ta kuma tabbatar da shi, amma saboda rashin sanin doka su rika cewa wai za’a kwacewa gwamna mulki to wallahi ba zamu lamunci wadancan kalaman ba”.

Hon. Musa Iliyasu Kwankwaso ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da yayi da jaridar kadaura24.
Ya ce tun da kotun sauraren kararrakin zaben gwamnan kano ta yanke hukunci yan kwankwasiyya suke ta karajin cewa za’a kwace musu Mulki, wanda kuma wannan abun da suke yi ya sabawa doka, tunda dai Kotu ce da kanta ta yanke hukunci akan batun bai kamata su rika fadin irin wannan kalamai ba.
Rashin adalci a shari’ar zaɓen Kano na iya haddasa tashin hankali a Africa- NNPPk
Musa Iliyasu Kwankwaso ya kuma zargin cewa abubuwan da yan kwankwasiyya suke yi na shirya zanga-zanga ya sabawa doka, saboda sun ɗaukaka ƙara kan hukuncin da kotun daukaka kara ya yanke zuwa kotun ƙoli, don haka kamata yayi su jira hukunci kotu na ƙarshe ba su rika barazanar tashin hankali ba .
Kotun Ɗaukaka Kara Tace Zaɓen Dan Majalisar Kunchi/Tsanyawa Bai Kammala ba
” Ina so na sanar da duk al’ummar cewa duk wannan abubuwan da yan kwankwasiyya suke yi Shure-Shure ne da bai taba hana mutuwa ba, tafiya ce sun tafiya, don haka ma nake kira ga Abba Kabir Yusuf da ya sallami mata da matasa tun da na sami labarin ya kwashe kayansa daga cikin gidan gwamnatin jihar kano baki daya.