Rashin adalci a shari’ar zaɓen Kano na iya haddasa tashin hankali a Africa- NNPPk

Date:

Jam’iyyar adawa ta NNPP a Najeriya ta ce hana ta kwace mata zaben da ta ci a jihar Kano, zai iya janyo tashin hankalin da zai yaɗu zuwa sauran ƙasahen Afirka.

Wata sanarwa da mukaddashin shugaban jam’iyyar na ƙasa, Abba Kawu Ali, ya fitar, kuma babban jami’i mai binciken kuɗi na jam’iyyar, Ladipo Johnson ya karanta a gaban ofisoshin jakadancin Kasashen Yamma ranar Laraba, NNPP ta yi ikirarin cewa akwai alamun da ke nuna cewa ana yunkurin yi wa zaben mafi rinjayen al’ummar Kano zagon kasa.

‘Ya’yan jam’iyyar suna ci gaba da zanga-zanga a Kano tun bayan hukuncin kotun daukaka kara da ya sake tabbatar da soke nasarar gwamnan NNPP, Abba Kabir Yusuf.

A ranar Laraba kuma, magoya bayan jam’iyyar sun yi zanga-zanga zuwa ofisoshin Tarayyar Turai da ofishin jakadancin Amurka da na Birtaniya da kuma Hukumar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Afirka ta Yamma (Ecowas).

Suna dai nuna ɓacin-rai ne kan hukuncin zaɓen gwamnan Kano da kotun korafin zaɓe da kuma ta ɗaukaka ƙara suka yanke a kan zaben gwamnan jihar Kano, da ya bai wa Nasir Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya, gaskiya.

Kotun Ƙoli ta yanke hukunci kan amfani da tsofaffin kuɗi a Nigeria

Ladipo Johnson ya ce jam’iyyar ba ta kallon takardar hukuncin kotun ɗaukaka ƙara da wasa, “kuma za mu yi duk abin da ya kamata bisa tsarin doka domin ƙwato abin da duniya ta sani cewa namu ne.”

“Yayin da NNPP ta garzaya zuwa Kotun Koli don bin kadi, mun damu da batun zaman lafiya, musamman na jihar Kano da kuma arewacin Najeriya baki-ɗaya. Don haka, muna son Kotun Koli ta yi adalci wajen dawowa al’ummar jihar Kano da gwamna Abba Kabir Yusuf, nasararsu.

“Yayin da muka je kotun karshe, hankula sun tashi a Kano. Kowane lungu-lungu da sako na jihar na cike da ɓacin rai, inda batun hukuncin kotun ya zama batun da ake tattaunawa a ko’ina, musamman a tituna, ofisohi, da gidaje,” in ji NNPP.

Ta kuma ce tana son faɗa wa shugabannin duniya cewa abin da ake shirin yi, ba abu ne mai kyau ga Najeriya kaɗai ba, har ma da Afirka da kuma duniya baki-ɗaya.

“Yunkurin kwace wa al’umma nasara a Kano, zai haifar da sakamako a kan al’amuran siyasa da tattalin arziki da kuma rayuwar mutanen jihar,” in ji jam’iyyar.

NNPP ta kuma yi kira ga masu ruwa da tsaki ciki har da mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, su janyo hankalin shugaban ƙasa da Kotun Koli wajen tabbatar da cewa an yi wa jam’iyyar da kuma al’ummar Kano, adalci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related