Daga Isa Ahmad Getso
Shugaban jam’iyyar APC na Nigeria, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana rasuwar fitaccen Daraktan Fina-finan Kannywood, Aminu Surajo Bono a matsayin rashi ga harkokin nishadi a Nigeria.
Dr. Ganduje wanda ya bayyana kaduwarsa game da rasuwar fitaccen jarumin, Inda ya ce ya rasu a daidai lokacin da masana’antar ke matukar bukatarsa.

Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da babban Sakataren yada labaran Shugaban jam’iyyar APC na Ƙasa Edwin Olofu ya sanyawa hannu kuma aka aikowa kadaura24.
“Bono ya yi tsayuwar daka domin ganin masana’antar Kannywood ta cigaba saboda jajircewarsa wajen bunkasa dabi’u da halaye na gari na al’ummar Hausa-Fulani “.
Yanzu-Yanzu: Kannywood ta yi Rashin Babban Darakta
Sanarwar tace Ganduje ya ce a lokacin rayuwarsa Aminu S Bono yayi amfani da baiwa da fikirar da Allah ya bashi wajen kawo cigaba mai tarin yawa masana’antar Kannywood, wanda hakan yasa al’umma da dama suka amfana.
Ganduje ya ce “Ina so in yi amfani da wannan lokacin wajen mika ta’aziyyata ga iyalansa da abokan sana’arsa na Kannywood, bisa rasuwar Aminu S Bono guda cikin daraktoci masu fikira a masana’antar Kannywood.”

Shugaban jam’iyyar APC na kasa ya ce, “Dole ne mu yarda cewa rasuwar Aminu Surajo Bono ta haifar da gibi a harkar nishadantarwa, kuma tabbas za’a jima ba’a cike gibin ba.
Dakta Ganduje ya yi addu’ar Allah ya gafarta wa Aminu S Bono ya sa aljanna ta zamo makomarsa ya kuma baiwa Iyalansa da yan Kannywood hakurin jure wanann gagarumin rashin.