‘Ƴan sanda za su ɗauki mataki kan masu son tayar da hargitsi a Kano

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Rundunar ƴan sandan Najeriya reshen jihar Kano ta ce za ta ɗauki tsattsauran mataki kan duk wadanda suke yunƙurin tayar da zaune tsaye bayan hukuncin da kotu ta yanke kan shari’ar zaɓen gwamnan jihar.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da rundunar ƴan sandar ta fitar yau Litinin ta hannun mai magana da yawunta a jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa.

Talla

Sanarwar ta ce ta yi gargaɗin ne “bayan samun wasu bayanai da ke nuna cewa akwai wasu ƙungiyoyin magoya bayan wasu jam’iyyu da ke yunƙurin shirya zanga-zanga kan titunan birnin (Kano) domin nuna ɓacin rai kan hukuncin kotun ɗaukaka ƙara game da zaɓen gwamnan jihar.

Shari’ar Gwamnan Kano: Ku marawa duk wanda Allah ya baiwa nasara a kotu baya – Kungiyar NILOWV

Sanarwar ta ƙara da cewa “bayanai sun ce waɗanda ke shirya zanga-zangar na so ne su dakatar da harkoki a jihar ta Kano wanda hakan zai iya tayar da zaune tsaye.”

Talla

A ranar juma’ar da ta gabata ne kotun ɗaukaka ƙara a Abuja ta bai wa Nasir Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC nasara a zaɓen gwamnan jihaR ta Kano, inda ta soke nasarar gwamna mai ci Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP.

Hukuncin kotun ya ce Abba bai cancanci zama ɗan takarar gwamna ba saboda rashin cika wasu ƙa’idoji.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...