Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Babban Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa, ya bayyana kwarin guiwar ganin nasarar aikin hajjin 2024.
A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar Sulaiman Dederi ya aikowa kadaura24, yace da yake jawabi a shirin Barka da Hansti na gidan rediyon Freedom, Alhaji Danbappa ya tabbatar wa jama’a cewa ana shirye-shiryen da suka dace domin gudanar da aikin hajjin cikin nasara.

Alhaji Laminu Danbappa, ya yi tsokaci kan matsalolin da suka shafi aikin hajjin shekarar da ta gabata, inda ya danganta duk wasu kura-kurai da shirye-shiryen da gwamnatin da ta shude ta yi.
Kotu ta bada izinin a liƙe takardar sammaci a Ƙofar Gidan Mawaƙi Rarara
Ya kuma jaddada kudirin shugabannin yanzu na ganin an gudanar da aikin Hajji cikin nasara a shekarar 2024.
“Kalubalan da aka fuskanta a aikin hajjin da ya gabata sun samo asali ne sakamakon shawarwarin da gwamnatin da ta shude ta yanke, Ina tabbatar maka muna bakin kokarinmu wajen ganin mun gyara wadannan matsaloli tare da tabbatar da ganin an samu saukin aikin hajji ga daukacin mahalarta Hajjin a shekarar 2024.” Inji Alhaji Danbappa.

Babban daraktan ya nuna jin dadinsa da irin goyon bayan da Gwamna Abba Kabir Yusuf yake ba shi, inda ya bayyana kokarin hadin gwiwar da ake yi na inganta aikin hajjin gaba daya ga maniyyata.
Ya kuma jaddada kudirin gwamnatin jihar na samar da kayan aiki da tallafi don tabbatar da gudanar da aikin hajji cikin nasara.