Dakile Harin Boko Haram: SEDSAC ta Yabawa Sojoji da DSS a Kano

Date:

Daga Zainab Muhammad

Wata kungiya dake take kokarin kare dimokuradiyya da samar da daidaiko a tsakanin al’umma wato SEDSAD ta yabawa Rundunar sojin Nigeria da hukumar tsaro ya farin kaya Saboda yadda suka dakile kokarin kungiyar Bako Haram na Kai wasu hare-haren ta’addaci a jihar kano a makon da ya gabata.
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito a ranar Juma’ar data gabata Rundunar Sojin Nigeria dake Kano da Hukumar tsaron farin kaya ta DSS sun fitar da wata sanarwar da suka ce sun dakile hare-haren ta’addaci da kungiyar Boko Haram ta shirya kaddamarwa a Kano.
Talla
Hakan na kunshe ne ta Cikin wata sanarwa da babban Daraktan kungiyar Com. Umar Hamisu Kofar Na’isa ya sanyawa hannu kuma aka aikowa kadaura24.
SEDSAC tace jami’an tsaron sun yi abun da ya dace na kokarin daƙile duk wani ta’addaci, maimakon a bayan da sai an Aikata laifin sannan a zo a Rika kokarin nemo Masu laifin.
” Ya kamata sake dagewa wajen yin addu’o’in samun zaman Lafiya a jihar kano da kasa baki daya don cigaban al’amura a Kasar “. SEDSAC
Sanarwar ta bukaci al’ummar jihar kano da Nigeria baki daya da su cigaba da baiwa jami’an tsaro hadin kai ta hanyar sanar da su duk wani motsi da basu aminta da shi ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...