Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Shari’ar Zaɓen Gwamnan Jihar Adamawa

Date:

Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa

 

Kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Adamawa a ranar Asabar ta tabbatar da Umaru Fintiri a matsayin zababben gwamnan jihar a zaben gwamna da za aka yi a watan Maris na 2023.

Bayan zaben gwamnan Adamawa wanda ya janyo aka tafi zagaye na biyu da aka sami cece-kuce, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana Fintiri a matsayin wanda ya lashe zaben.

Talla

A karshen zaɓen da aka kammala a watan Afrilu, Fintiri, na jam’iyyar PDP, ya samu kuri’u 430,861, inda ya doke Aisha ‘Binani’ Dahiru ta jam’iyyar APC wadda ta samu kuri’u 398,738.

Gwamnatin Kano ta Bayyana Dalilanta na Ciyo Bashin Naira Miliyan Dubu 4

Binani da wasu ’yan takara sun kai kara kotun suna neman ta soke nasarar Fintiri, amma kotun a ranar Asabar ta tabbatar da nasarar gwamnan mai ci a karo na biyu.

Tun da farko kwamishinan zabe na jihar Adamawa, Hudu Yunusa-Ari, ya shigar da cece-kuce bayan kammala zaben da aka gudanar a ranar 15 ga watan Afrilun 2023, inda ya bayyana ‘Binani’ a matsayin wadda ta lashe zaben yayin da ake tsaka da tattara sakamakon zaben.

Lamarin ya sa INEC ta soke sanarwar Yunusa-Ari tare da dakatar da shi yayin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba da umarnin gudanar da cikakken bincike kan kwamishinan zaben .

Daga nan ne INEC ta kammala zaben kuma ta sanar da Fintiri a matsayin wanda ya yi nasara a zaben .

Talla

Daga baya an kama Yunusa-Ari aka mika shi ga ‘yan sanda domin gurfanar da shi gaban kuliya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026

Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria ...

Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jihar Kano ta...

Idan mu ka rungumi Addu’o’i ba abun da Amurka za ta iya yiwa Nigeria – SKY

Shahararren ɗan kasuwa a Kano, Alhaji Kabiru Sani Kwangila...

Shugaban APC na Kano Abdullahi Abbas ya Magantu Kan Zargin raba Ramat da Kujerarsa

Shugaban jam’iyyar APC na Jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas,...