Kwankwaso@67: Gwamnan Kano Abba Kabir Ya Kaddamar Da Cibiyar Nazarin Al-Qur’ani

Date:

Daga Sani Idris Maiwaya

 

A ci gaba da bikin cikar Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso shekaru 67 a duniya, Gwamna Abba Kabir Yusuf a jiya (Asabar) ya kaddamar da wata cibiya ta karatun kur’ani da bincike mai suna Majidadi Institute for Qur’an Research and Advancement (MIQRA) da aka sadaukar da ita ga Marigayi Alhaji Musa Sale Kwankwaso a gidan Kwankwaso dake Miller road Kano.

Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yabawa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da ya yi nagartattun tsare-tsare da zasu ciyar da addinin musulunci gaba, inda ya ce an samar da cibiyar ne a lokacin da ake bukatar ta duba da dimbin makarantun Tsangaya da Islamiyya da ake da su jihar, akwai bukatar a shigar da su cikin tsarin Makarantu na yau da kullun don magance matsalolin almajirai da ke yawo a kan tituna.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban Sakataren yada labaran gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya sanyawa hannu kuma ya aikowa kadaura24.

Talla

Alhaji Abba Kabir ya kara da cewa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya samu nasarori da dama a lokacin gwamnatinsa ta fannin raya addinin musulunci inda ya bada misali da gyaran masallatan Juma’a da aka yi a fadin jihar da kuma kafa Makarantun Islama a kananan hukumomi 44 da kuma wasu manyan makarantu. ya koka da yadda gwamnatin da ta shude ta ki baiwa Makarantun kulawar data dace.

Gwamna ya yi alkawarin kammala Makarantun da aka yi watsi da su sannan kuma yace zai umurci Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kano domin ta fara daukar ɗalibai dob fara aikin gadan-gadan.

Rusau: Kotu Ta Gargadi Gwamnatin Kano Bisa Kokarin Bijirewa Umarnin Kotu

A nasa jawabin, Sen. Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce an kafa MIQRA ne domin horar da ma’abota haddar Alkur’ani mai girma maza da mata da kuma basu horo mai zurfi don ba su takardar shaidar kammala makarantun firamare da sakandare domin share musu hanyar shiga jami’o’i .

Ya kuma tabbatar da cewa a shirye yake ya yi duk abin da ya kamata don cibiyar ta yi aiki yadda ya dace domin baiwa dalibanta dama su binciko abubuwan da dama domin amfanin su da ma al’umma baki daya.

Abubuwan da Gwamnatin Kano ke yi Yanzu Shure-Shure ne da ba ya hana mutuwa – Dr. J Y

Ya yaba da jajircewar Gwamnan Jihar Alhaji Abba Kabir Yusuf na bullo da tsare-tsare wadanda suke da tasiri kai tsaye ga rayuwar al’ummar jihar Kano.

Talla

Malamai da dama daga ciki da wajen jihar sun yaba wa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso bisa yadda ya yi kyakkyawan shirin da zai zama daya daga cikin dabarun magance matsalar barace-baracen almajarai da ke addabar jihohi da dama a arewacin kasar nan.

Mataimakin gwamnan jihar, Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo, kakakin majalisar dokokin jihar Rt Hon. Ismail Jibril Falgore, Kwamishinoni da sauran manyan jami’an gwamnatin Kano na daga cikin manyan jami’an da suka halarci taron.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...