Daga Abubakar Sa’eed Sulaiman
Fitacciyar jarumar masana’antar finafinan Hausa ta Kannywood, Binta Ola ta rasu a safiyar yau Laraba.
Rahotanni sun bayyana cewa marigayiyar ta rasu ne bayan ta kammala shirye-shiryen Maulidi da za ta gudanar yau .

Wata majiya ta kusa da marigayiyar ta ce ta rasu ne da misalin ƙarfe uku na dare” bayan kamala ayyukan Mauludin da zata gabatar da safiya yau Laraba.”
An yi jana’izar ta da misalin ƙarfe 10:00 na safe a gidan ta da ke sabuwar unguwa, Ƙofar Ƙaura Santa a Jihar Katsina.
