Gwamnatinmu ba za ta sake karɓo bashi ba – Tinubu

Date:

 

Gwamnatin Najeriya ta ce ba ta da niyyar sake karɓo bashi a ciki ko wajen ƙasar ba, bayan cire tallafin man fetur da dunƙule tsarin canjin kuɗaɗen waje.

 

Ministan kuɗi da harkokin tattalin arziƙi, Cif Wale Edun ne ya bayyana haka a ƙarshen taron Majalisar Zartarwar Ƙasar na farko ranar Litinin a Abuja.

Talla

Ya ce amfanin da aka samu daga cire tallafin man fetur, za a zuba shi a ɓangarori daban-daban da za su taimaka wajen bunƙasa kuɗaɗen shiga ga gwamnati da inganta kasuwanci a cikin gida da kuma samun zuba jari daga ƙetare.

Bai Kamata Gwamnatin Kano ta yi Auren Zawarawa a Wannan Lokacin ba – Shitu Sani Marshall

BBC ta rawaito Wale Edun ya ce bayan ƙarin kuɗin shigar da aka samu sakamakon cire tallafin man fetur, an tsara matakan fitar da tallafin rage raɗaɗi na taƙaitaccen wa’adi da matsakaici da kuma dogon lokacin.

Ya jaddada cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na muradin farfaɗo da tattalin arziƙin Najeriya daga mawuyacin halin da yake ciki nan da wani ɗan lokaci.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya kuma ruwaito ministar masana’antu da kasuwanci da harkokin zuba jari, Doris Uzoka-Anite na cewa tuni har an fara samun masu tayin zuwa Najeriya don zuba jari a fannoni daban-daban na tattalin arziƙin ƙasar ciki har da ɓangaren man fetur da iskar gas da lafiya da haƙar ma’adanbai da kuma noma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...