Tallafawa manoma zai taimaka wajen rage tsadar rayuwa a Nigeria – Abubakar Usman Tabanni

Date:

Daga Shehu Hussaini Getso

 

Wani fitaccen manomi a yankin karamar hukumar Gwarzo a jihar Kano Alhaji Abubakar Usman Tabanni ya bukaci Gwamnatin tarayya da gwamnatin jihar Kano da su duba girman Allah suyi duk mai yuwuwa wajen taimakawa manoma da  daukacin al’umma domin ragewa al’umma radadi bisa samun kai a cikin mawuyacin Hali.

Ya ce a lokacin irin wannan babu wani fanni da zai fatattaki fatara da talauci da Yunwa da kaka-nikayi da kuma bada ayyukan yi fiye da fannin Noma, to a cewar sa duk da Muhimmancin fannin, a bana manoma sun sayi takin zamani da dan karen tsada haka ga yan kwadago suma.

Talla

Abubakar Usman ya yi rokon ne a madadin sauran manoman jihar Kano a zantawarsa da Kadaura24 a Kano.

Musa Iliyasu Kwankwaso ya maka gwamnatin kano da wata hukuma a gaban kotu

Usman Tabanni ya ce duk da a bana shi yayi matukar kokarin ganin ya noma gonakinsa kamar yadda ya Saba, amma kuma a hannu guda a kowacce rana yana samun mabuka akalla goma da suke zuwa wajensa domin neman tallafin abinci wanda hakan yake nuna yadda alumma me cikin mawuyacin hali.

Ya ce babban abinda ya kamata gwamnatoci suyi shine su samar da kyakkyawan tsarin tallafawa manoma da tallafawa alumma Baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...

Abdulmumin Kofa ya koma APC tare da bayyana goyon bayansa ga Tinubu

Abdulmumin Jibri Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru...

Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026

Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria ...