Emefiele bai bayyana a Kotu ba

Date:

 

An sake fuskantar wani tsaiko a shirin gurfanar da gwamnan babban bankin Najeriya da aka dakatar, Godwin Emefiele a gaban kotu, dangane da zargin karkatar da naira biliyan 6.9.

 

Babbar Kotun tarayya da ke Abuja ba ta lissafa shari’ar da ake yi wa Emefiele cikin shari’un da za ta saurara yau Laraba ba.

Talla

Lauyoyin Emefiele da hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), wadanda su ne masu gabatar da kara, ba su halarci zaman kotun ba.

Musa Iliyasu Kwankwaso ya maka gwamnatin kano da wata hukuma a gaban kotu

Ba a dai bayar da dalilin da ya sa shari’ar ba ta cikin jerin shari’un da za a saurara a kotun ba.

 

Hukumar DSS dai ba ta mayar da martani ga tambayoyin da BBC ta yi ba game da wannan lamari.

Tallafawa manoma zai taimaka wajen rage tsadar rayuwa a Nigeria – Abubakar Usman Tabanni

A ranar Alhamis din da ta gabata, Emefiele ya bayyana a kotun amma kotun ta ɗage ƙarar saboda Sa’adatu Yaro, wata ma’aikaciyar babban bankin kasar, kuma wadda ke fuskantar tuhuma tare da Emefiele ba ta bayyana a kotun ba.

 

Wannan ne ya sa mai shari’a Hamza Mu’azu, ya dage sauraron ƙarar zuwa ranar 23 ga watan Agusta.

 

Yaro da Emefiele suna fuskantar tuhume-tuhume 20 daga hukumar DSS, da suka hada da ” zamba da hadin baki da bayar da cin hanci da rashawa ga abokan hulda.

 

Ana tuhumar Mista Emefiele da bai wa Sa’adatu Yaro, wadda take darakta a April 1616 Investment Ltd, wani kamfani da ake zargi da alaka da lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...