Daga Aisha Aliyu Umar
Shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS na gudanar da wani taro yau Alhamis a Abuja kan halin da ake ciki a jamhuriyar Nijar.
Shugabannin za su yanke shawara kan matakin da za su dauka na gaba bayan jerin shawarwari da suka baiwa gwamnatin mulkin soja a Nijar na maido da mulkin dimokuradiyya a Kasa.

Shugaba Bola Tinubu, wanda shi ne shugaban kungiyar ECOWAS a halin yanzu yana karbar bakuncin shugabannin a fadar gwamnatin tarayya.
Wani fitaccen hukunci da aka yanke a baya a kan shugabannin shi ne yin amfani da karfin soji, bayan wa’adin kwanaki bakwai da aka baiwa gwamnatin mulkin da ta hambarar da shugaba Mohamed Bazoum.
Dogaro da kai: Falakin Shinkafi ya ɗauki nauyin koyawa Daliban makarantar Shekara 230 Sana’o’i
Kwanaki shida bayan bikin ranar 26 ga watan Yuli, shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS a wani taro da suka yi a Abuja, sun yi kira da a gaggauta sakin Bazoum a matsayin halastaccen shugaban kasa da gwamnatin Jamhuriyar Nijar.
Shugabannin sun yi kakkausar suka kan juyin mulkin da aka yi a Nijar, da tsare Bazoum ba bisa ka’ida ba, da kuma ‘yan uwa da gwamnatinsa.