Daga Ibrahim Abubakar Diso
Hukumar jin dadin alhazai ta jihar kano ta kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan wasu alhazai da suka rasu a kasa mai sarki yayin gudanar da ibadar aikin hajjin bana.
Kadaura24 ta rawaito Babban daraktan hukumar Alh , Laminu Rabiu Danbappa shi ne ya jagoranci tawagar daraktoci hukumar domin zuwa taaziyar.

Tunda fari dai tawagar ta ziyarci kauyen gago Rikadawa dake karamar hukumar Madobi inda aka yiwa iyalam Hajiya Hadiza Ismail ta’aziyya , bayan nan aka gabatar musu da kayan abinci da kudi wanda hukumar ta bayan ga iyalan marigayiyar.
A jawabin shugaban hukumar Alh. Laminu Rabi’u, yace marigayiyar ta rasu a birnin Makka kuma anyi mata sallah a masallacin Harami, sannan yayin musu ta’aziyya tare da yiwa mamaciyar addu’o’in samun rahamar Allah (S W A).
Juyin Mulkin Nijar: Muhammad Bazoum ya bayyana halin da ya shiga a hannun sojojin Nijar
Daya daga cikin dangin marigayiyar yace murgayiyar bata da da ko jika , amma ya nemi gwamnatin jiihar kano data yi musu rijiyar burtsatse domin a cigaba da tunawa da murgayiyar,kuma nan take Alh Laminu Rabiu ya amsa wannan bukata.
Daga bisani tawagar ta kai ziyara Garin Rimin Gado domin yin ta’aziyya ga iyalan mai unguwa Dan Azumi mai unguwar Zangon Dan Audu dake Rimin Gado wanda shi ma Allah ya karbi ransa a kasa mai sarki bayan gajeriyar jinya da yayi fama da ita, inda anan ma aka gabatar a addu’a ga mamacin sannan aka mika musu abinci da kudi.
Shugaban Majalisar Dattawan Nigeria ya yi subul da baka an wasu kudade
Haka zaluka tawagar takai ta’aziyya ga iyalan margayi, Alh Shitu Inuwa Gunduwawa dake karamar hukumar Gezawa wanda Allah ya karbi ransa a kasa mai tsarki , bayan ya kammala aikin hajjinsa, Babban daraktan hukumar jindadi alhazai ta jihar kano , Alh. Laminu Rabiu Dan bappa ya gabatarwa da iyalinsa kayan abinci da kudi.
Bayan nan tawagar taje karamar hukumar Gaya inda ta gana da iyala Umar Mustapha wanda yake fama da rashin lafiya, inda a yanzu haka yana karbar magani a kasa mai tsarki, Alh. Laminu Rabi’u ya tabbabatarwa da iyalansa cewa da zarar ya dada samun lafiya za a dawo dashi gida Nigeria, sannan ya gabatar musu da kayan abinci da kudi.