Bama goyon bayan ECOWAS ta yi amfani da karfin soji don warware matsalar Nijar – KCSF

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Gamayyar kungiyoyin fararen hula na jihar Kano (Kano civil society forum), sun fitar da budaddiyar wasika zuwa ga shugaban kasa Bola Ahmad Tunubu Kan rikicin Jamhuriyar Nijer da Kungiyar ECOWAS, bayan Juyin mulki.

 

Da yake bayyana makasudin fitar da wasikar yayin ganawarsa da manema labarai a kano, Shugaban gamayyar kungiyoyin fararen hular na jihar Kano Ambasada Ibrahim A Wayya, yace sunyi hakan ne don bayyana matsayar su, akan barazanar daukar matakan soji da kungiyar ECOWAS ke shirin yi akan Nijer.

Talla

Yace la’akari da nauyin da suke dashi na su bayyana matsayarsu da kuma ra’ayinsu kan abinda ke faruwa tsakanin kasar Nijer da kuma sauran kasashen Afrika, Wayya yace akwai bukatar kungiyar ECOWAS Karkashin Shugaban ta Bola Ahmad Tunubu, su yi taka tsantsan wajen daukar Mataki na soji domin warware rikicin jamhuriyar Nijer.

Yanzu-Yanzu: Gwamnan Kano ya nada mataimaka na musamman guda 42

Kazalika Wayya ya kara da cewa matsayar su itace bayar da shawarar kaucewa afkawa sojojin Nijar da yaki, yana mai cewa kamata yayi abi hanyoyin diflomasiyya da fahimtar juna wajen dawo da mulkin farar hula a kasar ta Nijar.

Da dumi-dumi: Akpabio ya bayyana sunayen shugabannin kwamitocin majalisar Dattawa

Daga karshe gamayyar kungiyoyin fararen hular na jihar Kano, sun ce yin amfani da karfin soji a kasar Nijar zai haifar da mummunan tasiri ga Arewacin Nigeria da sauran ƙasashen Afrika.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...

Abdulmumin Kofa ya koma APC tare da bayyana goyon bayansa ga Tinubu

Abdulmumin Jibri Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru...

Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026

Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria ...