Zargin Zagon Kasa: NNPP ta dakatar da sakataren ta na ƙasa

Date:

Daga Abdulrashid B Imam

 

Jam’iyyar NNPP ta dakatar da sakataren ta na kasa, Oladipupo Olayokun bisa zargin yi wa jam’iyyar zagon-ƙasa.

Dakatarwar na kunshe ne a cikin wata wasika da aka aike wa Mista Olayokun, mai dauke da kwanan wata 6 ga watan Agusta mai taken; “Sanarwar dakatarwa”.

Shugabannin jam’iyar na Ward 5 na karamar hukumar Abeokuta ta Kudu a jihar Ogun ne su ka dakatar da Olayokun, wanda kuma mamba ne a kwamitin ƙoli na jam’iyyar na kasa.

Talla

Wasikar wacce ke dauke da laifukan sa, ta samu sa hannun shugabanni 25 alna shiyyar, da suka hada da sauran mambobin mazabu 25.

Da dumi-dumi: Abba Gida-gida ya yi sabbin nade-naden shugabannin ma’aikatu 15

An aikawa shugaban kasa na jam’iyyar NNPP a zaben da ya gabata, Rabiu Kwankwaso, da kuma wanda ya kafa jam’iyyar, Boniface Aniebonam, kwafi na wasikar.

Daily Nigeria ta tawaito Shugabannin sun kuma zargi Sakataren jam’iyyar da yin sakaci da aiki tare da karfafa bangaranci a cikin jam’iyyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dan Majalisar tarayya daga Kano ya fice daga jam’iyyar NNPP

Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Kano Municipal, Injiniya Sagir...

Abin mamaki: Barawo ya sace Motar dake cikin ayarin motocin gidan gwamnatin Kano

Wani barawon mota ya kutsa cikin gidan gwamnatin jihar...

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...