Zamu Fara Kama ‘yan Adaidata Sahun dake Amfani da Gas Maimakon Man fetur – KAROTA

Date:

Daga Zainab Kabir Kundila

 

Hukumar kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa wato Karota tace za ta kama duk Adaidai Sahun da ke amfani da Gas mai makon fetur.

 

Ya bayyana cewa duba da irin haɗarin da gas ɗin ke da shi, zai iya fashewa ta kai ga rasa rai.

Talla

Shugaban Hukumar KAROTA Engr. Faisal Mahmud Kabir ne ya bayyana haka a Ranar Laraba.

“Nau’in gas ɗin da direbobin ke amfani da shi ba shi ne irin wadanda ake amfani da shi a ababen hawa ba”. Inji Faisal

Da dumi-dumi: Masu Zanga-Zanga Sun Ɓalle Ƙofar Majalisa

Yace a saboda wadancan dalilai, ya zama wajibi Hukumar ta kama duk wani matuƙi da aka samu yana amfani da gas ɗin maimakon Fetur

A wani cigaban kuma, shugaban Hukumar KAROTA ya ce an haramtawa jami’an KAROTA yin amfani da Gora a kan titin Kano.

Yace daga cikin nau’in horon sanin makamar aiki da ake baiwa jami’an za su iya gudanar da aikin su ba tare da amfani da Gora ba.

A cewarsa yin amfani da Gora ya saɓa da dokar da ta kafa Hukumar ta shekarar 2012.

Yace babu wani sashin doka da ya bayyana inda jami’an KAROTA za su yi amfani da Gora, “don haka ba za mu sauka daga tsarin doka mu yi abinda ya saɓa da tsarin doka ba

Ya ƙara da cewa ƙwarewar jami’i da iya mu’amalarsa da jama’a ita ce za ta taimaka masa a bakin aikinsa a mai makon amfani da gora.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Iftila’i: An tsinci gawar wata dattijuwa mai shekaru 96 cikin rami masai a Kano

A ranar Alhamis al’ummar ƙauyen Sarai da ke ƙaramar...

Na riga Kwankwaso shiga harkokin Siyasa – Sanata Barau Jibrin

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya...

Jaridun Amurka sun bankado Tsare-tsare uku da sojojin Amurka ke yi don tunkarar Najeriya

Rahotanni daga wasu jaridun Amurka na bayyana cewa rundunar...

Dalibai 22 sun kammala karatu da daraja ta 1 a bikin yaye ɗalibai na farko na Jami’ar Baba-Ahmed Kano

Jami’ar Baba-Ahmed, Kano ta gudanar da bikin yaye ɗalibai...