Daga Auwalu Alhassan Kademi
A yau Larabar ne kungiyar kwadago ta Najeriya NLC ta gudanar da zaman lumana duk fadin kasar don nuna adawa da cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi .
A jihar kano ma an gudanar da zanga-zangar inda kungiyar NLC ta jagoranci sauran kungiyoyin farar hula da kungiyar dalibai da Sauran domin yin zanga-zangar, sai dai masu zanga-zangar sun yi kakkausasan kalamai da kuma yin watsi da tallafin da gwamnatin tarayya tace zata baiwa yan kasar, tare da yin kira da a dawo a gaggawa dawo da tallafin man fetur.
Masu zanga-zangar da suka yi dafifi da misalin karfe 7:00 na safe a dakin karatu na jihar da ke kan titin Ahmadu Bello, sun yi tattaki zuwa gidan gwamnatin jihar kano domin mikawa gwamnatin kokensu don ita Kuma ta mikawa gwamnatin tarayya.

Masu Zanga-Zangar sun rika daga alluna Masu dauke da rubutu kala-kala dake nuna adawa da manufofin Shugaban kasa Bola Tinubu.
Yanzu-Yanzu: Tinubu ya Aikawa majalisa sunayen ministoci a karo na biyu
Kafin a kai gidan gwamnati, wakilin shugaban NLC, Dokta Muntaka Yusahu ya zargi shugaba Tinubu da yin aiki a karkashin asusun lamuni na duniya (IMF) wanda hakan ya gurgunta tattalin arzikin kasa.
Dokta Yusahu wanda ya koka da rashin samun wadataccan albashin ma’aikata da karin kudin makaranta da kuma tsadar rayuwa a Nigeria sakamakon cire tallafin man fetur, ya koka da abin da ya bayyana a matsayin tsarin mulkin mallaka a Najeriya.
Juyin Mulkin Nijar: Manyan Hafsan Sojoji na kasashen Yammacin Afirka Suna Ganawa a Abuja
A lokacin da yake mika sakon kungiyar ga gwamnatin jihar Kano, shugaban kungiyar NLC na jihar Kano, Kwamared Kabiru Inuwa ya nuna damuwarsa kan gazawar gwamnatin tarayya wajen cika alkawuran yakin neman zaben da ta yiwa al’ummar Nigeria.
Inuwa ya koka da yadda cire tallafin ke ci gaba da tsananta rayuwar al’ummar jihar Kano saboda yawan jama’a, inda ya yi kira da a dauki matakin gaggawa don fitar da al’umma daga cikin mawuyacin halin da akai .
“Muna gudanar da zanga-zangar lumana kamar yadda uwar kungiyar ta umurci mu yi, don nuna rashin jin dadin ‘yan Najeriya kan manufofin gwamnatin tarayya na musgunawa talakawa sakamakon cire tallafin man fetur,” in ji Inuwa.
Shugaban ya cire tallafin man fetur a ranar da aka rantsar da shi – matakin da mutane da yawa suka ce yana cutar da al’umma .
Da yake jawabi ga dimbin jama’ar da suka hallara a kofar shiga gwamnatin kano, sakataren gwamnatin jihar, Dakta Abdullahi Baffa Bichi ya ce gwamnatin jihar ba ta da wani sabani na aiki da ma’aikata, sannan yayi alkawarin zasu cigaba da kyautata alakar.
Yayin da yake yabawa da yadda aka gudanar da zanga-zangar lumanar, Baffa Bichi ya yi alkawarin isar da sakon zanga-zangar ga gwamnatin tarayya.