Juyin Mulkin Nijar: Manyan Hafsan Sojoji na kasashen Yammacin Afirka Suna Ganawa a Abuja

Date:

Daga Isa Ahmad Getso

 

Manyan hafsoshin soji daga wasu kasashen yammacin Afirka sun isa hedikwatar tsaro da ke Abuja, domin wata ganawa mai karfi kan ayyukan gwamnatin mulkin soja a Jamhuriyar Nijar.

 

Rahotannin da kadaura24 ta samu ya tabbatar da cewa kujerun da aka ware wa shugabannin sojojin Mali da Guinea Bissau da Nijar da Burkina Faso a halin yanzu babu kowa.

Talla

Hafsoshin sojojin da ke ganawar a halin yanzu sun hada da na kasashen Togo, Saliyo, Senegal, Nigeria, Ghana, Liberia, Guinea, Gambia, Cote’Divoire, Cape Verde da Jamhuriyar Benin.

Da dumi-dumi: Masu Zanga-Zanga Sun Ɓalle Ƙofar Majalisa

Shugaban kungiyar ta ECOWAS, Janar Christopher Musa ne ke jagorantar taron.

A ranar Lahadin da ta gabata ne kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS ta bai wa sojojin Nijar wa’adin mako guda su mayar was shugaba Bazoum mukamin sa ko kungiyar ta ɗauki matakin amfani da sojoji akan su .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...