Daga Rahama Umar Kwaru
Kungiyar kwadagon da ta kunshi kungiyoyin kwadagon Najeriya NLC da TUC ta ce za ta sake nazarin matakin fara yajin aikin gama gari a ranar Laraba 2 ga watan Agusta, 2023.
An shirya fara yajin aikin ne da zanga-zanga a gobe laraba 2 ga watan ugusta.

Bayan zama da kwamitin da shugaban kasa kafa kan bada tallafin rage radadin cire tallafin mai a Abuja ranar Talata, Emma Ugbaja, babban sakatare na kungiyar NLC, ya ce sun yi maraba da matakan da shugaba Bola Tinubu ya bayyana ya dauka duk da cewa akwai bukatar ya kara .
Yajin aiki: Majalisar Dattawa za ta gana da gwamnatin tarayya da kungiyar ƙwadago
Ugbaja ya ce kungiyar kwadago za ta tuntubi mambobinta domin cimma matsaya kan mataki na gaba kafin wayewar garin Laraba.
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito cewa kungiyar NLC ta shirya shiga yajin aiki da zanga-zangar lumana domin nuna kin Amincewarsu da matakin da shugaban kasa ya dauka na janye tallafin man fetur a Nigeria.