Da dumi-dumi: Kungiyar ƙwadago ta bayyana matsayarta ta ƙarshe akan zanga-zangar gobe

Date:

Daga Aliyu Danbala Gwarzo

 

Kungiyar Kwadago ta Najeriya NLC, ta bukaci ‘yan Najeriya da su yi watsi da labarin yiwuwar dakatar da yajin aikin da ta shirya yi a fadin kasar, wanda aka shirya farawa ranar Laraba.

 

A daren ranar Talata, kungiyar a cikin wata sanarwa mai cike da rudani mai dauke da sa hannun shugabanta na kasa, Joe Ajaero, ta ce za a gudanar da zanga-zangar kamar yadda aka tsara a manyan biranen kasar.

Talla

Kadaura24 ta rawaito tun da farko a wata ganawa da manema labarai a fadar shugaban kasa, babban sakataren kungiyar ta NLC, Emmanuel Ugboaja, ya bayyana cewa majalisar na iya sake duba matsayar ta a kan shirin yajin aikin, wanda kuma bayanin na Ugboaja ya haifar da cece-kuce a fadin kasar.

Yajin aiki: Majalisar Dattawa za ta gana da gwamnatin tarayya da kungiyar ƙwadago

Sanarwar wacce aka wallafa a sahihin shafin kungiyar NLC na Twitter, kungiyar ta ce, “Ku yi watsi da jita-jita ta karya, NLC kungiya ce mai haɗin kai kuma mai ƙarfi don haka muna bada tabbacin za a gudanar da zanga-zanga a gobe Laraba a duk fadin Nigeria.”

Hakazalika, mataimakin shugaban kungiyar NLC, Titus Amba, ya bayyana cewa babu wani sabon ci gaba da aka samu biyo bayan jawabin da shugaban kasa, Bola Tinubu ya yi a yammacin ranar Litinin.

A halin yanzu, NLC na neman a gaggauta sauya duk wasu manufofi da gwamnatin Tinubu ta bullo da su wadanda suka haifar matsin rayuwa ga yan kasa, kamar karin farashin man fetur, karin kudin makarantar gwamnati, sakin albashin malaman jami’o’i da ma’aikata da aka hana na tsawon watanni takwas da dai sauransu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jihar Kano ta...

Idan mu ka rungumi Addu’o’i ba abun da Amurka za ta iya yiwa Nigeria – SKY

Shahararren ɗan kasuwa a Kano, Alhaji Kabiru Sani Kwangila...

Shugaban APC na Kano Abdullahi Abbas ya Magantu Kan Zargin raba Ramat da Kujerarsa

Shugaban jam’iyyar APC na Jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas,...

Iftila’i: An tsinci gawar wata dattijuwa mai shekaru 96 cikin rami masai a Kano

A ranar Alhamis al’ummar ƙauyen Sarai da ke ƙaramar...