ECOWAS ta baiwa sojojin Nijar wa’adin mako guda su mayar da Bazoum matsayin shugaban kasar

Date:

Daga Sani Idris Maiwaya

 

Mambobin kungiyar  raya kasashen Africa ta ECOWAS, a ranar Lahadi, sun ba da wa’adin kwanaki bakwai ga sojojin Nijar da su mayar da kundin tsarin mulki da hambararren shugaban kasar Muhammed Bazoum kan mukaminsa.

 

Hakan ya biyo bayan wani taro na musamman da shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS suka yi a fadar gwamnati da ke Abuja, domin tattauna abubuwan da ke faruwa a Jamhuriyar Nijar.

Talla

A yayin da kungiyar ta amince da Bazoum a matsayin halastaccen shugaban kasar ta Nijar, kungiyar ta kuma sanya dokar rufe filaye da kan iyakoki, tare da dakatar da zirga-zirgar jiragen sama na kasuwanci tsakanin Nijar da kasashe mambobin kungiyar ECOWAS.

Yanzu-Yanzu: Sojojin Nijar sun Bayyana Sabon Shugaban Kasar

Da yake sanar da matakin, shugaban hukumar ta ECOWAS, Omar Touray, ya ce dukkanin hafsoshin tsaron kasashen kungiyar za su ci gaba da gudanar da wani taron gaggawa don tsara dabarun aiwatar da ayyukan soji na maido da Bazoum kan mukaminsa.

Ya ce kungiyar ta ECOWAS za ta dauki dukkan matakan da suka dace don maido da kundin tsarin mulki a Jamhuriyar Nijar.

Irin waɗannan matakan na iya haɗawa da amfani da ƙarfi.

“Don haka, hafsoshin sojojin ECOWAS za su gana cikin gaggawa.”

Da yake sanar da takunkumin tattalin arziki, Touray ya ce ECOWAS ta amince da “dakatar da duk wata huldar kasuwanci da makamashu da hada-hadar kudi tsakanin kasashen kungiyar ECOWAS da Nijar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Iftila’i: An tsinci gawar wata dattijuwa mai shekaru 96 cikin rami masai a Kano

A ranar Alhamis al’ummar ƙauyen Sarai da ke ƙaramar...

Na riga Kwankwaso shiga harkokin Siyasa – Sanata Barau Jibrin

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya...

Jaridun Amurka sun bankado Tsare-tsare uku da sojojin Amurka ke yi don tunkarar Najeriya

Rahotanni daga wasu jaridun Amurka na bayyana cewa rundunar...

Dalibai 22 sun kammala karatu da daraja ta 1 a bikin yaye ɗalibai na farko na Jami’ar Baba-Ahmed Kano

Jami’ar Baba-Ahmed, Kano ta gudanar da bikin yaye ɗalibai...