Zargin Tauye Hakki: Al’ummar Garin Zabuwa Sun Nemi Sarkin Gaya da Gwamnan Kano su Cire Mai Unguwarsu

Date:

Daga Rabi’u Usman

 

Al’ummar garin zabuwa Dawakiji dake cikin karamar hukumar Dawakin Kudu sun gudanar da zanga-zangar lumana domin nuna ɓacin ransu da kuma neman mahukunta su tsige mai Unguwar su bisa wasu zarge-zarge da suke yi a kansa .

Daga cikin zarge-zargen akwai cewa mai unguwar yana yin amfani da ƙarfin kujerar sa yana yiwa mutane tara ba tare da wani laifi ba.

 

Ko a kwanakin baya sai da wata mata da takai kara ya nemi ta biya, amma da tace bata da kudi duk da haka sai da ta siyar da akuya sannan ta biya tarar, sannan kuma mai unguwar baya mutunta mutanen garin zabuwa dake ƙarƙashin ƙasar Dagacin Dawakiji a karamar hukumar Dawakin Kudu”. Inji Wani mazaunin garin da ya nemi a boye sunansa

Talla

Al’ummar garin suka ce tun a baya sun zargi mai unguwar su Alhaji Auwalu Nuhu da hada baki da wasu mutane wajen kwace musu gonakin da suke tunkaho da su, wanda hakan ya haifar da rikici a tsakanin mutanen garin da mai Unguwar.

 

Kadaura24 ta ruwaito cewar, daga akalla mutanen da sukai zanga-zangar kuma suke so a cire mai Unguwar garin nasu na Zabuwa sun kai sama da mutane 200, inda suka rubuta takarda suka kuma sanyawa hannu dukkanin su.

Al’adun Bahaushe: Shin ko kun San Al’adar Bahaushe ta zuwa gida rainon ciki da haihuwa ?

Yanzu haka dai un fara bayar da takardun mu ga Mai Martaba Sarkin Gaya, da ofishin Hakimin karamar hukumar Dawakin Kudu, ofishin sakataren gwamnatin jihar kano, da shugaban majalisar dokokin jihar kano, sai Kwamishinan ‘yan sandan Kano da sauran hukumomi daban-daban duk dai don a Samar musu sauki ta hanyar raba su da wancan mai unguwa.

 

Bayan jin korafin Mutane garin na zabuwa hakan tasa jaridar Kadaura24 ta tuntubi mai unguwa Alhaji Auwalu Nuhu Zabuwa don Jin ta bakinsa dangane da koken mutanen garin zabuwa akan maganar gonakin nasu, da kuma koke akan suna bukatar a sauke shi daga mai unguwa.

Inganta Rayuwar matasa : Shekarau ya baiwa gwamnatin tarayya da na jihohi shawara

Sai dai mai Unguwa Alhaji Auwalu Nuhu Zabuwa yace bazai iya cewa komai ba akan batun, har sai ya samu umarni daga Hakimin karamar hukumar Dawakin Kudu.

A baya ma kadaura24 ta tuntubi shugaban karamar hukumar Dawakin kudu Hon. Nasiru Ibrahim Matage akan wannan korafi na mutanen garin Zabuwa, sai dai shugaban yace wannan korafi bai je teburin sa ba, amma dai yace zai bincika ya gano asalin abinda ke faruwa.

Tun da farko dai wani kamfani mai suna Kano Maradi Standard Goarge ne zai fara gudanar da aikin titin dogo daya taso daga Maidugurin jihar Borno ya shigo kano wanda za’a yi tashar sa a garin Zabuwa, daga nan kuma ya tashi zuwa maradin Jamhuriyar Nijar

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...