Mun Gano Kabilanci da Rashin Kuɗi ne yasa Fina-finan Kannywood Basa Karade Nigeria – Ado Gidan Dabino

Date:

Daga Abdulmajid Habib Isa Tukuntawa

 

Shugaban kungiyar Masana’antar fina-finai ta MOPAN reshen na jihar Kano  Alhaji Ado Ahmad Gidan Dabino, ya koka da yanayin da masa masana’antar shirya fina-finai Hausa ta kanywood take ciki a nan kano da kuma Arewa cin Nageria .

 

“Daga cikin manyan matsalolin da harkar fim take fuskanta akwai rashin kasuwa yadda ya kamata da kuma masu satar fasaha sai kuma chanza musu ma’anar film dinsu zuwa wata alkibilar ta daban”.

Talla

Kadaura24 ta rawaito Ado Ahmad Gidan Dabino ya bayyana hakan ne yayin wani taro na yini biyu da Kungiyar ta shirya domin duba irin kalubalen da sha’anin harkar fim ke ciki a Arewacin Nigeria.

 

Yace kungiyar MOPAN da sauran masu ruwa da tsari sun bada tabbacin yin duk mai yiyuwa wajen ganin an kawo ƙarshen matsalolin da suka dabaibaye Masana’antar Kannywood da arewacin Nigeria baki daya .

Yunkurin rushe gidaje: Kotu ta ci tarar gwamnatin Kano

Gidan dabino ya kuma musanta zargin da ake yi musu na cewa jarumai da sauran masu harkar fim a Arewacin Nigeria basu da kwarewar da ta dace, wanda hakan ne yasa takwarar fina-finsu basa karade nageria baki daya, sai dai kawai su tsaya a arewacin Nageria .

 

“Kabilancin da suke fuskanta daga gurin abokan sana’ar su na kudancin Nageria ne yasa fina-finan hausa basa iya zuwa har cen kudancin Nigeria, da kuma karanchin kudi ga masu shirya film a Arewacin Nigeria”. Inji Gidan Dabino

 

Gidan Dabino yace zasu ɗauki matakan da suka dace domin magance matsalolin da suke cikin harkar film a jihar kano dama kasa baki daya.

Yace samun cikakken hadin kai tsakaninsu da gwamnati tare kuma da basu damar tantance duk wani film da zai fita bayan an kammala shi kafin fitarsa ga al’umma.

A nasa jawabin Sakataren kungiyar ta MOPAN reshen jihar kano Kamal S Alkali yace a yayin taron an fito da matsalolin Masu tarin yawa da Masana’antar take fuskanta, kuma an bada shawarwarin hanyoyin da za’a bi domin warware su.

Masu ruwa da tsaki a harkar fim a kano da kasa baki daya ne suka sami hallarta taron cikinsu harda shugaban kungiyar MOPAN ta kasa baki daya Alh Ahmad Sarari.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Tinubu ya Iso Kano domin ta’aziyyar Dantata

Shugaban Nigeria Bola Ahmad Tinubu ya iso jihar Kano...

ALGON ta Kano Sa’adatu Soja ta sami sabon matsayi a kungiyar ALGON ta Ƙasa

Daga: Aliyu Danbala Gwarzo. Shugabar karamar hukumar Tudunwada kuma ALGON...

Da dumi-dumi: Tinubu zai zo Kano

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu zai zo Kano ranar...

Tinubu ya sauya sunan jami’ar Maiduguri zuwa Sunan Muhd Buhari

Shugaba Bola Tinubu ya sauya sunan Jami'ar Maiduguri zuwa...