Shari’ar zaɓen gwamnan Kano: Rashin bayyanar Shaidu Abba Gida-gida a Kotu yasa hana shi fara kariya

Date:

Daga Aliyu Danbala Gwarzo

 

Rashin halartar shaidu uku na Abba Kabir-Yusuf na jam’iyyar NNPP ranar juma’ar nan, ya hana shi fara yin kariya a Shari’ar zaɓen gwamnan kano da jam’iyyar APC ta shigar a gaban kotun sauraron kararrakin zabe ta jihar Kano.

 

NAN ta ruwaito cewa masu shigar da kara jam’iyyar APC na kalubalantar INEC kan ayyana Abba Kabir-Yusuf na NNPP a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gudanar a ranar 18 ga Maris, 2023.

Talla

Wadanda APCn take kara sun hada da INEC, Abba Kabir-Yusuf da kuma jam’iyyar NNPP .

 

A lokacin da aka kira karar, Lauyan Abba Kabir-Yusuf, Mista Eyitayo Fatigun SAN, ya shaida wa kotun cewa shaidu ukun da suke son gabatar wa ba su sami damar halartar zaman Kotun ba.

Da dumi-dumi: Abba Gida-gida ya nada shugabannin wasu Ma’aikatun Lafiya a Kano

“Muna ba da hakuri saboda shaidun uku sun sami matsalar jirgin a kan hanyarsu ta zuwa Kano daga Abuja. Ya mai Shari’a muna neman a dage shari’a” inji Fatigun

 

Lauyan INEC, Emmanuel Osayomi da Lauyan NNPP, John Olusola SAN, ba su yi adawa da bukatar hakan ba.

 

Shi ma lauyan wanda ya shigar da kara, Offiong Offiong SAN, bai yi adawa da bukatar dage shari’ar da wanda ake kara na biyu ya nema ba.

 

Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito tun a ranar 15 ga watan Yuli Mai Kara wato jam’iyyar APC ta kammala gabatar da shaidu inda ta gabatar da shaidu 32, yayin da INEC a ranar 21 ga watan Yuli ta rufe karar ta ba tare da gabatar da shaida ko daya ba.

 

Mai shari’a Oluyemi Akintan-Osadebay ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 22 ga watan Yuli, domin wanda ake kara na biyu ya fara kariya .

 

NAN ta ruwaito cewa mai shigar da kara yana kuma rokon kotun da ta bayyana cewa NNPP ba ta da dan takara saboda Abba Kabir-Yusuf baya cikin rajistar masu kada kuri’a da suka mika wa INEC a lokacin zabe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamna Abba Ya Sanya Hannu Kan Dokar Kafa Gaya Polytechnic

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sanya...

Sojoji sun mikawa Tinubu Shawarwari yadda za a kawo karshen matsalar tsaron Nigeria

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya karɓi rahoton dakarun sojan...

Shugaba Tinubu ya sake nada Buba Marwa a matsayin shugaban NDLEA

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake tabbatar da nadin...

Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa Ya Koma Jam’iyyar APC a Hukumance

Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar...