Rundunar Soji ta Nigeria ta hallaka yan ta’adda 22 a katsina

Date:

Rundunar sojin sama ta Najeriya ta kashe akalla ‘yan bindiga 22 a ƙananan hukumomin Jibiya da Batsari a jihar Katsina da ke arewa maso yammacin ƙasar.

Wata majiya mai ƙarfi a rundunar sojin ta shaida wa PRNigeria cewa an kai harin ne a kan tsaunukan da ‘yan bindigar ke ɓoye, bayan samun bayan sirri da ke nuna cewa suna kitsa wani hari domin yin garkuwa da matafiya a kan hanyar Jibiya zuwa Katsina.

Jaridar PRNigeria ta ruwaito ce wa ‘yan bindigar – waɗanda galibinsu yaran riƙaƙƙen ɗan bindigar nan ne da aka kashe Abdulkareem Boss – an kashe su ne ranar Litinin, a wani hari ta sama da dakarun rundunar ‘Hadarin Daji’ mai yaki da ‘yan bindiga – a yankin arewa maso yammacin ƙasar – ta kai.

Talla

Majiyar ta ce ‘yan bindigar sun addabi al’umomin yankin, inda suke yin garkuwa da mazaunan wasu yankuna a ƙaramar hukumar Kankara.

Harin wanda ya yi sanadin mutuwar ‘yan bindiga da dama , ya kuma lalata sansanonin ‘yan bindigar.

A cikin watan Agustan 2022 ne dai rundunar sojin sama ta Najeriya ta kashe fitaccen ɗan bindigar nan mai suna Abdulkareem Boss tare da wasu daga cikin yaransa a wani hari ta sama da rundunar ta ƙaddamar kan maɓoyarsu a dajin Ruga da ke jihar Katsina.

Da dumi-dumi: Abba Gida-gida ya nada shugabannin wasu Ma’aikatun Lafiya a Kano

An zargi Abdulkareem da kitsi wani mummunan hari da ya yi sanadin kashe wani babban baturen ‘yan sanda a ƙaramar hukumar Dutsinma ranar 5 ga watan Yulin 2022.

Mai maganar da yawun rundunar sojin sama ta Najeriya Air Commodore Edward Gabkwet, wanda ya tabbatar da harin na ranar Litinin, ya ce babban hafsan sojin sama na ƙasar, Air Vice Marshal Hasan Abubakar, ya umarci dakarun sojin saman ƙasar da su haɗa kai da sauran jami’an tsaro domin kakkafe duka ‘yan ta’addan da kuma maɓoyarsu

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zargin Almundahana: ICPC zata gurfanar da shugaban hukumar zabe ta Kano da wasu mutum biyu

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta (ICPC)...

Dalilin da ya hana ni zuwa Kano tarbar Tinubu – Ganduje

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa,...

Shugaban RATTAWU na Kano ya taya sabbin shugabannin kungiyar na kasa murna

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Shugaban kungiyar ma’aikatan rediyo, Talabijin da...

Dalilina na ziyartar gwamnan Kano Abba – Inuwa Waya

Daga Rahama Umar Kwaru Tsohon Wanda ya nemi Zama Dan...