Daga Aisha Aliyu Umar
A yanzu haka dai taron Majalisar Tattalin Arzikin Kasa (NEC) yana gudana a zauren Majalisar da ke Abuja ranar Alhamis.

Taron wanda mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ke jagoranta, ya samu halartar gwamnonin jihohi 36 na tarayyar Nigeria, da daraktan kungiyar gwamnonin Najeriya, da masu ruwa da tsaki daga bankin duniya da sauran hukumomin gwamnati.
Da dumi-dumi: Abba Gida-gida ya nada shugabannin wasu Ma’aikatun Lafiya a Kano
Wannan dai shi ne taro na biyu na majalisar kuma ana sa ran za ta tattauna kan shirin baiwa al’umma tallafi, sakamakon cire tallafin man fetur da kuma hauhawar farashin man fetur a kwanakin baya.
Shugaba Bola Tinubu ne ya ba da umarnin bitar kuma ya kamata ya kasance kan gaba a ajandar taron da sauran batutuwan da zasu tattuna.
Taron dai na cikin wani zama na sirri.