Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
Wani kwararren likita a asibitin koyarwa na Malam Aminu kano Dr . Aminu Abdullahi Taura ya bukaci likitoci masu tasowa da su rika mai da hankali wajen yin bincike don samun kwarewa a fannonin da suke aiki musamman ma likitocin kwakwalwa da Cutar farfadiya.
” Mun gayyato Kwararrun likitoci daga cikin da wajeb Nigeria don gabatar da makaloli wadanda zasu zaburar da matasan likitoci su fahimci muhimmancin bincike don Kara inganta lafiyar al’umma, musamman ta fannin cututtukan kwakwalwa da cutar farfadiya”.

Dr. Amina Taura ya bayyana hakan ne yayin wata taron karawa juna Sabi da aka Shiryawa likitocin kwakwalwa da Cutar farfadiya, wanda Asibitin koyarwa na Malam Aminu kano da Jami’ar Bayero da wasu jami’o’i da asibitoci suka ɗauki nauyin gabatar a Kano.
Da dumi-dumi: Abba Gida-gida ya nada shugabannin wasu Ma’aikatun Lafiya a Kano
Dr. Amina Taura yace muddin matasan likitoci suka tashi tsaye wajen yin bincike za’a sami saukin gano matsalolin da suke addabar al’umma da Kuma hanyoyin da za’a bi don magance su.
” Ina kira da likitocin da suka halarci wannan taron da su yi koyi da dumbin ililmin da aka koya musu domin inganta aikin su da kuma kula da lafiyar al’umma”. Inji Dr. Aminu Abdullahi Taura
Wasu likitoci da wakilin Kadaura24 ya zanta da su sun yabawa wadanda suka shirya taron, tare kuma da bada tabbacin zasu yi aiki da ilimin da suka samu a yayin taron wanda aka gudanar da shi a Kano.
Yayin taron Kwararrun likitoci da manyan Malamai daga jami’o’i daban-daban su gabatar da makaloli yayin taron.