Gwamnatin Kano ta yabawa Cibiyar Sarki Salman bisa yiwa Mutane sama da 1800 aikin idanu kyauta

Date:

Daga Kamal Umar Kurna

 

Gwamnatin jihar Kano ta jaddada kudirin ta na baiwa kungiyoyi masu zaman kan su na ciki da wajen kasar nan cikakken hadin kan daya kamata domin ciyar da fannin lafiya gaba a jihar .

 

Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusif ne ya bayyana hakan a wajen kaddamar da yiwa masu larurar ido da yawansu ya kai 1,818 aiki kyauta a asibitin Makka, Wanda cibiyar Sarki Salman na kasar Saudiyya ta dauki nauyin yi musu hadin gwiwa da gwamnatin jihar Kano.

Talla

Gwamna Abba Kabir wanda ya samu wakilcin Shugaban hukumar kwashe shara ta jihar nan Alhaji Ahmadu Haruna Zago yace cibiyar ta Sarki Salman ta jima tana yin irin wadannan ayyuka domin inganta rayuwar masu karamin karfi a fadin duniya baki daya.

Da dumi-dumi: Gwamnan Kano ya Baiwa Dan Wasan Hausa Mukami Mai Gwabi , Tare da Nada Wasu Mutane 13

” Babu shakka wanna aiki na kula da lafiyar al’umma ya zo daidai da kuɗirin gwamnatin kano na inganta fannin kula da lafiyar al’umma, don haka zamu cigaba da baiwa cibiyar hadin kai da goyon baya domin cigaba da bukasa aiyukan su a kano”. Inji Alh. Amadu Haruna zago

Da yake jawabi a wajen kaddamarwar kwamishinan lafiya na jihar Kano Dr Abubakar Yusif yace gwamnatin jihar Kano ce ta dauki nauyin tantance wadanda za’a yiwa aikin ta hanyar hada hannu da gidauniyar domin zakulo wadanda suka dace domin ayi musu aikin kyauta.

Tunda farko da yake nasa jawabin karamin jakadan kasar Saudiyya dake kano Khalil Ahmad Admawi yace Sarki Salman ya amince da gudanar da aikin ne a sassa da yawa na duniya domin taimakawa masu karamin karfi a tsakanin al’umma.

Ya kuma yabawa gwamnatin jihar kano da al’ummar jihar bisa hadin Kai da goyon bayan da suke baiwa cibiyar da Kasar Saudiyya baki daya, wajen gudanar da irin wadannan aiyuka na Jin kai ga masu karamin karfi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dan Majalisar tarayya daga Kano ya fice daga jam’iyyar NNPP

Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Kano Municipal, Injiniya Sagir...

Abin mamaki: Barawo ya sace Motar dake cikin ayarin motocin gidan gwamnatin Kano

Wani barawon mota ya kutsa cikin gidan gwamnatin jihar...

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...