Daga Aisha Aliyu Umar
A ranar labara 19 ga watan Yulin 2023 ne ake sa ran Majalisar Dattawa za ta karbi sunayen ministoci da Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai nada domin dafa masa wajen jagorantar ƙasar.

Magatakardar majalisar dattawan ne ya ce wannan bayanin na kunshe ne a cikin wata wasika da ya samu.
Yan Nigeria dai sun dade suna sauraron su wa shugaba Tinubu zai nada domin nadin nasu shi ne zai nuna alkiblar gwamnatin da kuma manufofin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu wajen magance dimbin kalubalen da ke fuskantar tattalin arzikin Nigeria.