Daga Kamal Umar Kurna
Shugaban hukumar kwashe shara ta jihar Kano Amb. Alhaji Ahmadu Haruna Zago ya bayyana bukatar dake akwai na samar da wani tsari tsakanin hukumar sa da shugabannin kasuwannin jihar nan a bangaren tsaftace kasuwannin.
Shugaban ya bayyana hakan ne lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a kasuwar kantin kwari, lokacin da ake gudanar da aikin kwashe sharar Wanda shine Karo na 4 a kasa da makwanni 2.

Dan zago yace hukumarsa da gwamnati ba za su cigaba da zura idanu da yawa daga cikin kasuwannin jihar nan suna cigaba da rufe tituna sanadin sharar da suke zubarwa a akan titunan ba.
Wasu daga cikin ‘yan kasuwar ta kwari sun bayyana cewa ana fito da sharar ne daga cikin kasuwar a tsakiyar dare da Kuma unguwar fagge ta yadda sai dai su wayi gari suga sharar ta toshe hanyar wucewa.
Dan zago yace duba da yadda gwamnati take kashe makudan kudade wajen aikin kwashe sharar akwai bukatar al’umma su bada cikakken hadin Kai da goyon baya domin samun nasarar da aka Sanya a gaba.